Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adamawa: Wasu ‘Yan Majalisu Biyu Sun Sauya Sheka Zuwa APC


Dakin Majalisar Jihar Adamawa
Dakin Majalisar Jihar Adamawa

Babbar Jam’iyyar adawa ta PDP ta rasa wasu ‘yan majalisun wakilai daga jihar Adamawa, batun da ya sake bude wata sabuwar dambarwa a jihar.

Cikin ‘yan Majalisun da suka sauya sheka suka bar jam’iyar PDP da takaisu kujerar da suke akai, har da ‘dan majalisar wakilai dake wakiltar mazabar Madagali da Michika Mr Adamu Kamale da kuma na majalisar dokokin jihar Mr Emmanuel Tsandu, koda yake jam’iyar PDP a jihar tace Allah ya raka taki gona.

Da yake zantawa da manema labarai jim kadan da bikin wankan tsarkin da aka yi musu, Mr Adamu Kamale ya danganta sauya shekar da rikicin shugabancin da ya dabaibayi jam’iyyar PDP a Najeriya.

To sai dai kuma shugabanin jam’iyar PDP a jihar sun ce su basu damu ba, Alhaji Sabo Garta, dake zama shugaban jam’iyar a yankin Michika yace Allah raka taki gona.

Shima da yake tsokaci sakataren wani bangare na jam’iyar PDP a jihar Adamawa Hon. Zira Tumba Gaye, ya ce cikinsu bai debi ruwa ba, tun da zama a jam’iyya ra’ayi ne kuma ra’ayi riga ce kowa da yadda yake sa tasa.

A Najeriya dai, sauya sheka ga wadanda aka zaba zuwa jam’iyyar da ke mulki ba sabon abu bane, koda yake ga yan siyasa irinsu Hon. Abdullahi Prembe, na ganin zata sauya zani a zaben shekarar 2019.

Yanzu dai lokaci ne kawai ke iya tabbatar da abin da shekarar 2019 za ta haifar, zaben sak za’a yi ko kuma na cancanta.

Domin karin bayani saurari rahotan Ibrahim Abdul’aziz.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:38 0:00

Facebook Forum

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG