Mataimakin gwamnan jihar Injiniya Haruna Manu, wanda ya wakilci gwamnan lokacin da yake mika tallafin ga shugaban kungiyar shugabannin kananan hukumomi ta ALGON, ya ce gwamnati na sane da ba kowa zai ci gajiyar tallafin ba, amma ya bukaci shugabannin kananan hukumomin da aka dankawa amanar rabon sa su tabbata ya isa ga wadanda aka yi tanadi domin su.
Wannan matakin na tallafawa marasa galihu musamman a wata mai alfarma inji malami a sashin koyar da addinin Musulumci a kwalejin horas da malamai na tarayya dake Yola Dokta Liman Bashir, sauke hakki ne da ya rataya a wuyan shugabannin.
Malamin ya yi kira ga talakawa da ba su da sukunin taimakawa junansu su zama masu addu’a ga magabatansu, su kuma kyautatawa juna da yawaita ziyara don su sami albarkar wannan wata na azumi. Yayin a daya bangaren ‘yan kasuwa inji Dokta Bashir Liman ya ce za su yi riba duniya da lahira idan ba su tsauwala mutane ta hanyar neman kazamar riba a wannan wata mai alfarma ba.
Kungiyar shugabannin kananan hukumumi ta jihar Taraba, ta bakin shugaban ta Hon. Stephen Ibrahim Agiya, wanda ya amshi tallafin kayan abincin buda-baki a madadin kungiyar ya yi alwashi tabbatar da ba a karkata ko da kwayar hatsi ba, tare da kamanta adalci wajen rabon.
Don tabbatar da tallafin ya kai ga sako-sakon jiha gwamnatin jihar Taraba ta yi tanadi na dakon kayan da jigilarsu don ta ga sun isa ga wadanda aka yi domin su.
Domin karin bayani ga rahoton Sanusi Adamu.
Facebook Forum