A bara dai an biya Naira Miliyan ‘daya da dubu goma sha biyar kudin kujerar, al’amarin da ke nuna cewa an sami ‘karin sama da Naira dubu ‘dari biyar a wannan karo.
Shugaban kungiyar Izala a Najeriya, Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya ce suna cikin barin rai akan wannan ‘kari, wanda ya ce a bara gwamnatin Najeriya ta tallafawa matafiya musamman ta bangaren canjin kudaden guzuri, kuma ya kamata a ce bana ma gwamnati ta taimakawa, a cewar Bala Lau.
A wannan karon babu maganar biyan kudin babbar kujera ko karama, gaba ‘daya lamarin guda ne. Alhaji Lawali Mohammed, shugaban kamfanin Shukura Bread, na ganin wannan farashi da aka saka yayi yawa ga masu niyyar tafiya aikin hajji. Inda yayi kira ga hukumar Alhazai da ta duba halin da ‘kasa da jama’ar cikinta ke ciki.
Yanzu haka dai hukumar jin dadin Alhazan ta bayar da wa’adin mako guda da kowanne maniyaci da ya fara bayar da kudin ajiya da ya cika sauran.
Shugaban hukumar Alhazan jihar Neja, Alhaji Idris Adamu, ya a bara gwamnatin tarayya ta taimakawa maniyyata wajen samun saukin Dalar Amurka, amma wannan shekara gwamnati ta ‘daga hannunta.
Ko baya ga kudin kujerar, yanzu haka kudin guzuri ya koma dalar Amurka ‘dari takwas, maimakon Dala dubu ‘daya zuwa dubu ‘daya da ‘dari biyar a baya.
Domin karin bayani ga rahotan Mustapha Nasiru Batsari.
Facebook Forum