Ranar Lahadi, hukumar zabe da ake kira CENI ta fara rajistar masu kada kuria’a a birnin Kinshasa mai kimanin mutane miliyan goma sha biyu, inda shugaban kasar Joseph Kabila ya zama na farko da aka yiwa rajista. Ana kyautata zaton za a dauki watanni uku ana rajistar masu kada kuri’a.
Jiya litinin, Muryar Amurka tayi hira da Providence Nsongo a wata mazabar dake makarantar sakantare ta lardin Burunb
Nsongo yace yazo ne domin sauke nauyin da ya rataya a wuyansa na dan kasa, ta wajen yin rajistar da zata bashi ikon daukar mataki a kan hukumomin siyasa da na gwamnati. Yace abinda ya dace ke nan ga al’ummar kasar Congo.
Sai dai galibin mutanen kasar basu tsammani za a gudanar da zaben bana.
Kofi Luakaviny ya shaidawa Muryar Amurka cewa, yana fata za a gudanar da zaben shekara ta dubu biyu da goma sha takwas, sabili da Kabila baya so ya sauka daga karagar mulki. Yace shugaban kasar yana kan kokarin mamaye Congo, yana daukar kansa tamkar wani allah a kasar.
Facebook Forum