Shugabannin Fulanin sun bayyana haka ne alokacin da suke ganawa da wata tawagar jami’an ofishin jakadancin kasar Amurka a Najeriya, domin gano bakin zaren warware rikicin Manoma da Makiyaya wanda ya ki ci yaki cinyewa.
Sarkin Fulanin Legas kuma jagoran Fulani a ganawar, Alhaji Mohammad Banbado, ya ce tun da Amurka ta shiga wannan magana hakan na nufin gwamnatin Najeriya ta kasa kenan, inda yake ganin tunda gwamnatin Amurka ta shiga maganar babu mamaki gwamnatin Najeriya ta mayar da hankali akan batun.
Wanan ganawa da akayi tsakanin Fulani da wakilan ofishin jakadancin Amurka, itace ta biyu kenan a kokarin da gwamnatin Amurka ke yi na warware rikicin. wanda masana harkokin tsaro da kungiyoyin sa kai ke ganin ya zama wajibi gwamnati ta tashi tsaye wajen magance shi.
Daya daga cikin shugabannin kungiyoyin sa kai da ke neman bakin zaren warware rikicin, Imam Shafi’u Abdulkareem, ya ce makasudin wannan taro shine na ganawa da shugabannin Fulani domin magance rikicin da yaki ci yaki cinyewa.
Alhaji Mohammad Kabir Lambar, shugaban kungiyar Miyetti Allah na jihohin yammacin Najeriya, yayi kira ga makiyaya da su tashi tsaye su baiwa shugabanninsu goyon baya, domin ganin an amince da kungiyoyin dake zuwa daga kasashen waje don taimakawa a sasanta.
Domin karin bayani saurari rahotan Babangida Jibrin.
Facebook Forum