Jakadan Amurka a Najeriya Richard Mills Junior ya ce babu wata hujja da za ta sa Amurka ta amince da zargin da ake ma Hukumar Raya Kasashe ta Amurka USAID cewa ita ke tallafa wa Kungiyar Boko Haram
Majalisar Dattawa ta dauki haramar yin bincike kan zargin da dan Majalisar Dokokin Amurka, Scott Perry, ya yi cewa Hukumar Gwamnatin Amurka mai Tallafa wa Kasashen Duniya, USAID, ita ce ta rika tallafa wa Kungiyar Boko Haram a Najeriya.
Majalisar Dokokin Tarayyar Najeriya ta amince da kasafin Kudin bana mafi girma sabanin yadda aka saba a watan Janairu zuwa Disamban kowacce shekara a baya.
Wata sanarwa da Ma'aikatar Harkokin Waje ta fitar mai dauke da sa hannun Mukaddashin mai magana da yawun ta, Kimiebi Imomotimi ta ce Najeriya ta zama kasa ta 9 da ta shiga Kungiyar BRICS a matsayin Kasa amintacciya da ta karbi goron gayyata domin hadin gwiwa da Kungiyar..
Majalisar dokokin Najeriya ta yi watsi da kasafin kudin Ma'aikatar yada labarai da wayar da kan al'umma ta kasa da dukkan hukumomin da ke karkashin ma'aikatar.
Malaman sun yi zargi sabuwar Majalisar Gudanarwar Jami'ar da kaucewa bin tsari wajen nada Farfesa Aisha Sani Maikudi a matsayin shugabar Jami'ar, said ai kuma awkai amma kuma akwai wani rukunin Malaman da suka ce zargin ba shi da tushe.
Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Najeriya (TCN) ya ba da sanarwar zai dauke wutar lantarki a wasu sassa na babban birnin tarayya Abuja, daga ranar 6 ga watan Janairu zuwa 20 ga wata na wannan shekara.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gabatar wa haddaden zaman Majalisar Kasa da Kasafin kudi da ya kai Naira Triliyan 47.9 wanda ya zama shi ne kasafin kudi mafi tsoka da aka taba yi a kasar.
An dauki tsauraran matakan tsaro a harabar Majalisar Dokokin kasar gabanin gabatar da kudurin kasafin kudin shekarar 2025 na Naira tiriliyan 47.916
Majalisar Dattawa ta yi amai ta lashe inda ta ce ba ta soke yin aiki kan kudurin sake fasalin haraji da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kawo mata ba.
Majalisar wakilai ta dauki wani mataki da wasu ke gani abin alheri ne bayan jin irin koke koken da suka rika tashi kan batun korar ma'aikata 1,000 da Babban Bankin Najeriya ya ce zai yi, yayinda kwararru a fanin tattalin arziki ke gani akwai bukatar kyakkyawan karatun ta natsu kan lamarin.
Domin Kari