Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dattawa Ta Yi Watsi Da Korafin Natasha


Sanata Natasha da Sanata Akpabio
Sanata Natasha da Sanata Akpabio

Abin da ya dauki hankali a wannan dambarwa shi ne a karon farko, shi da kansa Sanata Godswill Akpabio ya jagoranci zaman Majalisar a lokacin da Natasha ta gabatar da takardar korafin.

Sanata Natasha Akpoti Uduaghan ta mika wa Majalisar Dattawa takardar korafi kan zargin da ta yi wa Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio, cewa ya ci zarafinta, amma Shugaban Kwamitin jin koke-koke da kula da da'a, ladabi da kare hakkokin 'yan Majalisar, Neda Imasuen ya yi watsi da takardar korafin, kuma ya ba da hujjojin daukan wannan mataki.

Abin da ya dauki hankali a wannan dambarwa shi ne a karon farko, shi kanshi Sanata Godswill Akpabio ne ya jagoranci zaman Majalisar a lokacin da Natasha ta gabatar da takardar korafin da ita da kanta ta sa hannu, wanda yin haka a zauren Majalisar ya ba Akpabio daman yin bayani kan korafin cewa, wannan zargi da Sanata Natasha ta yi masa, karya ce mara tushe.

A cewar shi, bai taba yi mata wani abu na cin zarafi ba, kuma shi bai taba yi wa wata mace irin wannan cin zarafin ba.

Akpabio ya ce yana girmama mata domin yana da mata da 'ya'yansa hudu, kuma dukkan su mata ne. Saboda haka shi bai ci zarafin kowa ba kuma ba zai ci zarafin kowa ba.

Sanata Natasha da Sanata Akpabio
Sanata Natasha da Sanata Akpabio

Bayan wannan zaman da aka samu musayar yawu tsakanin Natasha da Akpabio, sai kwamitin kula da da'a da jin koke-koke, ladabi da kare hakkokin ‘yan Majalisa ya gayyaci Sanata Natasha domin ta yi wa kwamitin karin bayani, amma har zuwa karfe 5 na yamma agogon Najeriya, Sanata Natasha ba ta bayyana a gaban Kwamitin ba.

Shugaban Kwamitin ya yi wa manema labarai bayani yana cewa, sun yi watsi da wannan takardan korafi da Sanata Natasha ta kawo wa Majalisa domin bai bi ka'idojin da aka tanadar a cikin oda ta 40 karamin sashe na 4 na kundin tsarin mulkin Majalisar Dattawa ba.

Imasuen ya ce kundin tsarin mulkin Majalisa ya nuna cewa babu wani Sanata da zai iya gabatar da takardar koke ko korafi mai dauke da sa hannunsa da kansa.

Majalisar Dattawan Najeriya (Facebook/Majalisar Dattawa)
Majalisar Dattawan Najeriya (Facebook/Majalisar Dattawa)

Ya kara da jaddada cewa tunda Natasha ba ta amsa gayyatar kwamitin ba, kwamiti zai zauna ya yi nazari kan irin shawarwarin da ‘yan Majalisar dattawa za su bayar sannan su mika rahotonsu ga cikkakiyar Majalisar dattawa a yau alhamis.

Amma tsohon dan Majalisar dattawa daga Jihar Kano El-jibril Doguwa ya kawo shawara cewa, ya kamata a kawo karshen wannan dambarwa ta hanyar hikima, ta yadda ‘yan Majalisa za su kulle kansu su tattauna domin samun mafita.

El-jibril ya ce ita kuwa Natasha ya kamata ta yi amfani da bayanin da ake yi na lallashi domin a kai ga biyan bukata.

Ya kara da cewa lallashi wanda ake cewa “lobby” a turanci hanya ce ta tafiyar da dimokradiya a duniya baki daya ba a Najeriya kawai ba.

Saurari cikakken rahoton Medina Dauda daga Abuja:

Majalisar Dattawa Ta Yi Watsi Da Korafin Natasha.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:18 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG