'Yan Najeriya sun bayyana yunkurin da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ke yi na kara ciwo bashi a matsayin maida hannun agogo baya a fannin tattalin arziki
Masaan sun ce akwai bukatar kyakkyawan nazari kan hanyar shawo kan matsalar wutar lantarki a Najeriya, biyo bayan bayanin da Ministan Makamashi Adebayo Adelabu yayi cewa, Najeriya ana bukatar 'yan kasuwa su zuba jarin dala biliyan 10 domin a shawo kan matsalar wutar lantarki a kasar.
Batun dokar sake fasalin haraji da shugaba Bola Tinubu ya aika Majalisa ta ja cece-kuce a tsakanin 'yan Arewa, musamman wasu ‘yan Majalisa da wasu kungiyoyi masu zaman kansu, wadanda suka nuna cewa kudurin zai iya yin illa ga muradun Arewa, idan har aka amince ya zama doka.
Gwamnatin Najeriya ta bayyana niyyar ta fara samar da wutar lantarki na tsawon sa'o'i 20 a kullum, zuwa nan da shekara 2027.
Kamfanin wutar lantarki ya bayyana dalilin sake rugujewar tashar wutar lantarki ta kasa a karo na 12.
A yau Litinin ne Ministan babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja, Nyesom Wike ya kaddamar da yaki da mabarata, inda ya bayyana cewa jami'an tsaro za su fara kama su daga yau idan sun sake fitowa bara a titunan babban birnin.
Kamapanin bada wutar lantarkin ya ce 'yan ta'adda ne ke lalata hanyoyin bada wutar lantarki. Lamarin da ya jefa yankin arewacin Najeriya cikin duhu tsawon kwanaki.
Ezeh ya ce "lamarin ya shafi duk tashoshin TCN a fadin kasar, saboda haka babu wadatar wuta da za'a baiwa abokan hulda."
Majalisar Wakilan Najeriya ta nemi Jakadan Kasar Canada ya sa gwamnatin kasarsa ta yi bincike mai zurfi domin hukunta wata mata 'yar Najeriya mazauniyar garin Ontario mai suna Amaka Patience Sunnberger kan furucin da ta yi na nuna kiyayya a dandalin sada zumunta na tiktok.
Majalisar Wakilai ta yi kira ga Gwamnatin Tarraiya da ta dakatar da Shugaban Hukumar Kula da harkar man fetur ta Najeriya har sai an kammala binciken zarge-zargen da ake yi wa abinda ta kira "kalamai mara dadi da zai iya kashe wa kasar kasuwa" da shugaban hukumar ya yi.
Kwararru a fannin siyasa da gudanar da mulki a Najeriya sun bayyana ra'ayoyi mabanbanta kan janyewa daga tsayawa takara da shugaba Joe Biden ya yi, inda wasu ke gani ya yi abin da wasu kasashe za su yi koyi da shi.
Domin Kari