Yayin da sojojin Myanmar suke ci gaba da yaki da 'yancin fadi sonka, sojojin kasar ta Myanmar, sun bayyana kama wani tsohon ministan yada labarai a kasar.
China ta sanar cewa shugabancin jam'iyyar kwaminis na da mahimmiyar rawar da zai iya takawa a game da al'amuran kudade, a wurin babban taron da aka shirya don tattauna batutuwan da suka shafi samar da kudade da kuma kashe su wanda akayi a babban birnin kasar, Beijing
Wata gobara da ta tashi a wani daki da ake taron daurin aure a Arewacin Iraqi ta yi sanadin mutuwar sama da mutane 100 sannan wasu 150 sun jikkata a ranar Laraba, inda hukumomin suka yi gargadin yiwuwar karuwar alkaluman mace-macen.
Domin Kari