Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Manyan Kasashen Duniya Suka Yi Rige-Rigen Karfafa Dangantaka Da Kasashen Afirka A 2023


Shugabannin kasashen nahiyar Afirka
Shugabannin kasashen nahiyar Afirka

A cikin watannin 12 da suka gabata, shugabannin Afirka sun ziyarci hedkwatar Tarayyar Turai a Brussels da Indiya da Rasha da Amurka da Saudiyya da Afirka ta Kudu da kuma Turkiyya.

Nahiyar Afrika na ci gaba da daukan hankalin manyan kasashen duniya wadanda suke rige-rigen ganin sun kara dankon dangantakar siyasa da tattalin arziki da kasashe 54 da ke nahiyar.

A cikin watannin 12 da suka gabata, shugabannin Afirka sun ziyarci hedkwatar Tarayyar Turai a Brussels da Indiya da Rasha da Amurka da Saudiyya da Afirka ta Kudu da kuma Turkiyya.

Har ila yau, sun gana da Shugaban kasar Sin, Xi Jinging, a kasar Afirka ta Kudu, inda suka tattauna kan shirin samar da ababen more rayuwa na kasa Sin, da samar da kudade na sauyin yanayi da harkokin kasuwanci da yarjeniyoyin cinikayya da zaman lafiya da tsaro a duniya.

Ursula von der Leyen, hagu, shugabar kwamitin kungiyar Tarayyar Turai lokacin da take gaisawa da Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, dama, a taron G20 A Berlin a watan Nuwamba, 20, 2023.
Ursula von der Leyen, hagu, shugabar kwamitin kungiyar Tarayyar Turai lokacin da take gaisawa da Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, dama, a taron G20 A Berlin a watan Nuwamba, 20, 2023.

Farfesa Chacha Nyaigotti Chacha, kwararre kan harkokin diflomasiyya da huldar kasa da kasa, ya ce nahiyar Afirka na da muhimmiyar rawar da za ta taka a harkokin duniya kuma kasashe na da muradin yin hulda da nahiyar a fannoni da dama.

Ya ce “Suna son samar da dabaru kan yadda za su ci gaba da bai wa kasashen Afirka tabbacin cewa su abokanan ‘yan Afirka ne, saboda haka suna fatan kasashen Afirka za su ci gaba da hulda da su cikin lumana, kuma suna sa ran samun riba mai yawa na tattalin arziki da kyakkyawar fata a siyasance.”

Sai dai wasu masana sun bayyana wasu daga cikin tarukan da shugabannin kasashen Afirka ke halarta a matsayin wadanda ba su da tushe balle makama.

Shugaban Biden, dama, da Shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa
Shugaban Biden, dama, da Shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa

Yayin da rikici kamar yakin Rasha a Ukraine da yakin Isra’ila da Hamas ke gudana, masana harkokin siyasa sun ce taron kasa da kasa na samar da hanyar da wasu kasashe ke neman goyon bayan Afirka.

Paul Melly, mai ba da shawara ne ga Shirin Afirka a Chatham House da ke Burtaniya, wata kungiya mai bincike. Ya ce Afirka na iya yin tasiri a zauruka kamar na Majalisar Dinikin Duniya, inda kasashen ke kada kuri’a kan batutuwan siyasa da tsaro.

Ya ce “Akwai wata hujja mai sauki ta sarrafa alkaluma a Afirka dangane da yadda ake kidaya su, kuna kallon kuri’u 50 a Majalisar Dinikin Duniya, wanda hakan ke da babban tasiri. Akwai wasu nahiyoyi da suke da kasahe kadan a cikinsu.

Shugaban Rasha, Vladimir Putin, dama tare da Shugaban Kamaru Paul Biya, hagu
Shugaban Rasha, Vladimir Putin, dama tare da Shugaban Kamaru Paul Biya, hagu

Daya daga cikin abubuwa da suka yin fice a Afirka shi ne nahiya ce da ke da alamu na daukan matsaya ta bai-daya, wacce yawan kuri’unta suke da karfi da kuma karfin fada a ji a siyasance.”

Ya ce, “yawan hadin gwiwa yana da mahimmanci, kuma za ku iya samun tarurruka masu yawa kamar yadda ku ke so, za ku iya tattara albarkatu kamar yadda ku ke so, amma idan ba ku dace da daidai sosai ba, idana ana ganin yanayin ba shi da cikakkiyar girmamawa ko rashin son a zauna da saurari abin da shugabannin Afirka za su ce, wani lokaci za ku ga baya aiki.”

Masana sun ce cikin shekaru masu zuwa, suna sa ran za a samu karin kasashe da za su nemi yin hulda da Afirka. Ko da yake Chacha ya ce akwai bukatar kasashen nahiyar su kara dankon zumunci a tsakaninsu.

Ya ce “Za su tuna shekarar 2023 a matsayin shekarar da suka yi mu’amala da sauran kasashen duniya da na ketare, kuma zu su yi saurin koyar cudanya tsakanin su domin sauran shekaru masu zuwa su samu magana da murya daya.”

Shugaban Faransa, Emmanuel Macron
Shugaban Faransa, Emmanuel Macron

Wasu kasashe kamar Faransa, sun fadada yadda suke mu’amala da Afirka, ba wai kawai gayyato shugabanninta ba, har ma da matasanta, da mata da masu fafutuka da ‘yan kasuwa don kulla kyakkyawar alaka.

Sai dai ana zaman tankiya tsakanin Faransa da wasu kasashe da ta yi wa mulkin mallaka a Afirka.

Kasashen sun hada da Burkina Faso da Mali da Nijar, wadanda suka kori sojojin Faransa. An kuma yi juyin mulki a kasashen uku na Afirka, wadanda a baya bayan nan suka kulla kawancen tsaro da nufin yaki da masu ikirarin jihadi.

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG