A ranar 13 ga watan Janairu da mu ke ciki, kasashe 23 da ga nahiyar Afirka za su halarci kasan Ivorry Coast don fafatawa a gasar cin kofin nahiyar Afrika ta AFCON.
Wata sanarwa da Hukumar Kwallon Kafar Afirka ta CAF ta fitar ta yi bayani akan kudin da wadda ya lashe gasar da ma sauran da za su halarci gasar, za su samu.
Hukumar ta ce duk tawagar da ta lashe gasar ta bana za ta samu kyautar dala miliyan bakwai ($7M), kwatankwacin (Yuro Miliyan 6.4), a sanarwar da fitar a yau, Alhamis.
Hakazalika, wadanda suka yi rashin nasara a wasan kusa da na karshe za su samu dala miliyan biyu da rabi ($2.5M) kowanne, sannan kuma wadanda suka kai matakin kwata fainal za su samu dala miliyan 1 da dubu dari uku ($1.3M) kowanne su, a cewar sanarwar, wacce ba ta bayar da cikakkun bayanan kyautar kudaden da za’a bayar wa sauran kasashen da za su halarci gasar ba.
Mai masaukin baki Ivory Coast da sauran kasashe 23, ciki har da kasar Masar da ta lashe gasar sau bakwai, za su fuskanci kalubalen samun nasara a kasar Yammacin Afirka.
Ivory Coast, wacce ta lashen kofin sau biyu za ta kara da Guinea Bissau, ba tare da samun nasara ba a wasannin uku da suka buga a baya, a ranar 13 ga watan Janairu a wasan farko na bude gasar a filin wasa na Alassane Ouattara mai cin mutane 60,000 da ke Abijan.
AFP
Dandalin Mu Tattauna