Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bani Da Wata Alaka Da Kamfanin Intels – Atiku Abubakar


Atiku Abubakar
Atiku Abubakar

“Saboda haka, jita-jitar da ake yadawa cewar zan amfana da sake dawo da yarjejeniya tsakanin Intels da Gwamnatin Tarayya ba gaskiya ba ne, wannan bata suna da kage ne kawai.”

Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa bai da wata alaka da kamfanin dakon kaya na bakin teku wato Intels.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Atiku ya ce “Tun a watan Janairun 2021, na sayar da hannun jarina a kamfanin Intels ga babban kamfanin zuba jari na Orlean.”

Atiku ya ce “Matakan sayar da hannayen jarin da aka fara tun shekarar 2018, sun yi karfi a watan Disamban 2020. Kamfanin Intels ya sanar da ficewa ta daga daya daga kamfanin na sufurin man fetur da iskar gas, ma’ana ke nan wani ne a yanzu ya mallaki hannayen jarin."

A cewar Atiku “Tun daga wannan lokaci ba’a dawo da zuba jarin a kamfanin Intels da muka kafa ba tare da wasu ba. Don haka, babu dalilin da zai sa a yi tunanin cewa zan amfana da dawo da yarjejeniyar da ke tsakanin Intels da Gwamnatin Tarayya, wanda a baya gwamnatin ta soke yanzu kuma ta dawo da shi.”

Ya kara da cewa “Saboda haka, jita-jitar da ake yadawa cewar zan amfana da sake dawo da yarjejeniyar tsakanin Intels da Gwamnatin Tarayya ba gaskiya ba ne, wannan bata suna da kage ne kawai.”

Gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta dawowa da kamfanin Intels kwangilar sa bayan tsohuwar gwamnatin Buhari ta soke kwangilar a 2020.

Wani rahoto ya nuna cewa gwamnatin ta dau matakin ne don rufe duk hanyoyin da kudi ke sulalewa a sanadiyyar rashin aikin kamfanin.

A baya dai Atiku da kan sa ya taba fitowa fili ya nuna adawa da gwamnatin Buhari kan daukar wasu matakan zagon kasa a kan sa.

Tsohuwar shugabar hukumar kula da tashoshin teku Hadiza Bala Usman ta jagoranci soke kwangilar kamfanin Intels da zummar mika aikin ga wani kamfani amma hakan bai yiwu ba.

Dawo da aikin Intels na daga misalan irin yadda gwamnatin Tinubu ke soke wasu ayyuka da gwamnatin Buhari ta yanke matsaya a kai, da su ka hada da hana ba da dala wajen shigo da wasu hajoji 43 da yanzu babban banki ya dawo da hurumin ba da dalar.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG