Daya daga cikin mutane takwas da suka jikkata a harin na daren Juma'a, wanda aka kashe dalibai 38, ya mutu cikin dare, in ji Selevest Mapoze, magajin garin Mpondwe-Lhubiriha.
Shirin zauren matasa a wannan makon, ya yi bayani kan wani taro da aka yi a jihar Bauchi, inda matasa su ka tattauna kan abin da ya dace su (matasa) maida hankali a kai bayan kammala babban zaben Najeriya na 2023.
Zargin da tsohon jagoran masu tada kayar baya a yankin Niger Delta Asari Dokubo ya yi wa rundunar sojin Najeriya na cewa suna taka rawa wajen satar mai, na ci gaba da jan hankali.
Shugaban riko na karamar hukumar Mangu a jihar Filato Markus Artu, ya ce sun dakatar da duk zirga-zirgar motoci da babura in ban da jami’an tsaro da wadanda ke ayyuka na musamman.
A Najeriya, har yanzu ana ci gaba da kai wa wasu al'ummomi hare-hare musamman mazauna yankunan da ke fama da ‘yan bindiga. Wannan na zuwa ne a lokacin da ‘yan bindiga suka afka wasu garuruwa da ke karamar hukumar Illela a jihar Sokoto, inda suka kashe mutane da dama tare da sace dabbobi masu yawa.
Yajin aikin da masu dafa abinci a makarantu ke yi na iya tilasta wa yaran makaranta da ke cin gajiyar shirin ciyar da dalibai da gwamnatin Ghana ta bullo da shi zama da yunwa, da wasu rahotanni
Watanni shida bayan zarginta da hallaka gwamman makiyaya, rundunar sojojin saman Najeriya ta bada bahasi cewa ‘yan ta'adda ta halaka a wannan farmaki.
Babbar kotun jihar Kaduna ta yi barazanar bada umarnin kamo shugabannin hukumar makarantar horar da sojin Najeriya da ke Jaji matukar su ka ci gaba da taka umarnin kotun na barin al'ummomin yankin su je gonakinsu.
A shirin Nakasa na wannan makon muna jihar Agadez da ke yankin Arewacin Jamhuriyar Nijar inda muka tabo batun gudunmowar masu bukata ta musamman a sha’anin wasannin motsa jiki.
Yayin da wasu al'ummomi a Najeriya ke ci gaba da fuskantar hare-haren da suke tuhumar Fulani barayi ke kai wa, ita kuwa kungiyar Fulani ta kasa ta kara kokawa akan cin zarafi da ta ce ake yi wa Fulani a kasar.
Wani kwale-kwalen kamun kifi da ke dauke da bakin haure masu yunkurin isa Turai ya kife a ranar Laraba a gabar tekun Girka, kamar yadda hukumomin kasar suka bayyana.
Lamarin rashin tsaron dai ya kara ta'azzara a ‘yan kwanakin nan a jihar Nejan Najeriyar, al’amarin da ya jefa dubban mazauna yankunan karkara cikin yanayi na tashin hankali.
Rashin samun daidaito game da wanda zai jagoranci majalisar jihar ta Jigawa karo na takwas, shi ne ya haifar da tsaiko wajen rantsar da sabbin ‘yan majalisar ranar Talata.
Wani Mazaunin yankin da lamari ya faru Malam Muhammad Sani ya ce jirgin kwale-kwalen ya dauko wasu ‘yan biki ne daga kauyen Boti na yankin karamar hukumar Patigi ta jihar Kwara.
Domin Kari