WASHINGTON, D.C. - A ranar Lahadi ne wani gari da ke kan iyakar Uganda ya fara jana'izar wadanda suka mutu sakamakon wani mummunan hari da ake kyautata zaton 'yan tawaye masu tsattsauran ra’ayi ne suka kai shi a kan wata makaranta, harin da ya yi sanadin mutuwar mutane 42, mafi yawansu dalibai, yayin da jami'an tsaro suke kara daukar matakan sintiri a kan iyakar kasar da gabashin Congo.
"Galibin 'yan uwan wadanda suka rasa rayukansu sun kwashe gawarwakinsu daga dakin ajiye gawa,” in ji magajin garin.
Bayan daliban 38, wadanda harin ya shafa sun hada da wani mai gadin makarantar da wasu farar hula su uku. Akalla biyu daga cikinsu ‘yan gida daya ne, an yi jana’izarsu ranar Lahadi.
An kona wasu daliban ta yadda da wuya a gane su; an harbe wasu, wasu kuma aka sassare su har suka mutu, bayan da wasu ‘yan bindiga dauke da bindigogi da adduna suka kai hari a makarantar sakandare ta Lhubiriha, wadda ke da tazarar kilomita 2 (fiye da mil daya) daga kan iyakar Congo. Hukumomin Uganda sun yi imanin cewa an sace dalibai akalla shida, wadanda aka dauke su a matsayin masu dakon kaya aka maida su cikin jirgin dakon kaya.
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya yi Allah wadai da harin a cikin wata sanarwa, inda ya jaddada "muhimmancin hadin gwiwa, gami da inganta kawance a yanki, don magance matsalar tsaron kan iyaka tsakanin Congo da Uganda da kuma dawo da zaman lafiya mai dorewa a yankin."
An dora alhakin harin kan kungiyar mayakan ADF, wacce ba kasafai ta ke daukar alhakin kai hare-hare ba. Wadda kuma ta kulla alaka da kungiyar IS.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, martaninsa na farko a kan lamarin, shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni ya bayyana harin a matsayin "babban laifi, na ta'addanci mara amfani kuma," yana mai shan alwashin tura karin sojoji a gefen iyakar ta Uganda.
-AP