An sanya dokar ne biyo bayan wani yamutsi da ya kai ga rasa rai da jikkata wasu mutane.
Shugaban kungiyar matasan Mwaghavul, Sunday Dankaka Dawap, ya ce zargin da aka yi na cewa za a farma wadanda ke gudun hijira shi ne musabbabin tashin rikicin.
A makonnin da suka gabata an sami munanan hare-hare a karamar hukumar Mangu, da suka yi sanadin lakume rayukan mutane fiye da dari, dubban mutane kuma suka yi gudun hijira, lamarin da ya sanya fargaba da zargi a tsakanin mabambantan kabilu da addinai a yankin.
Shugaban kungiyar Miyetti Allah a karamar hukumar Mangu, Yahaya Bello Shanono, ya ce rikicin ya samo asali ne bayan da aka hallaka wani mai sana'ar achaba.
Kansilan Mangu Ward one, Kabiru Iliyasu, ya bukaci sarakuna da shugabannan al’umma da na addinai da su ja hankalin jama’a don a zauna lafiya.
Ko a ranar Jumma’ar da ta gabata ‘yan bindiga sun hallaka mutane takwas a yankin Fan da ke karamar hukumar Barikin Ladi.
Gwamnan jihar Filato Caleb Mutfwang, a wata sanarwa ya umurci jami’an tsaro da su tura karin jami’ansu don dakile tashin hankalin.
Sanarwar ta kuma ce gwamnati zata yi amfani da matakai dabam-dabam don kare al’ummar da ‘yan ta’adda suka mamaye yankunansu.
Tun farko rundunar ‘yan sanda ta ce ta tura jami’anta a yankunan da ke fama da tashin hankali don tabbatar da tsaro da kare dukiyoyin jama'a.
Saurari cikakken rahoto daga Zainab Babaji: