ABUJA, NIGERIA - Jim kadan bayan ya gana da shugaban kasa Bola Tinubu a fadar gwamnatin kasar da ke Abuja, Asari Dokubo ya zargi mayakan Najeriya da cewa su ne kanwa uwar gami wajen satar gurbataccen mai a kasar.
“Sojoji ne a kan gaba wajen satar mai, a saboda haka ya zama dole mu fada wa ‘yan Najeriya. Kashi casa'in da tara na satar danyen mai sojojin kasa da sojojin ruwa ke yi, sojin kasa da na ruwa na zura wa hukumar tsaron farin kaya ta Civil Defence ido, wadanda bisa doka su ya kamata su samar da tsaron bututun mai,'' a cewar Dokubo.
Ya kuma ce jami'an tsaron na karbar makudan kudi daga kamfanonin mai, amma abin bakin ciki ana tafka aika-aikar a ko ina, za ka ga ana jan mai kai tsaye daga bututun mai na hukuma bayan kuma kusan kowacce mita daya sai ka ga shingen sojin kasa ko na ruwa, amma barnar sai ci gaba ta ke yi.
Abin da ke faruwa a yankin Niger Delta cikin shekaru takwas din da suka gabata wani abu ne da ba a taba ganin irinsa ba a tarihin samar da mai a duniya, inda wasu tsiraru suka mamaye wuraren da ake hako man suke kuma tace shi ba bisa ka'ida ba.
Dokubo ya ce shugaban kasa ya tabbatar masa cewa zai dauki tsauraran matakai wajen dakatar da wannan barna ba tare da bata lokaci ba.
Muryar Amurka ta tuntubi rundunar mayakan ruwan kasar don jin martanin da zata mayar, amma nan take dai ba ta yi wani bayani ba.
Masana harkokin tsaro a kasar na ganin zargin da Asari Dokubo ya yi na bukatar karin bayani, musamman da ya ce babu shakka akwai wasu bata gari cikin sojoji da ke yin laifi.