Shirin Zauren Matasa har yanzu muna Bauchi ne inda matasa su ka taru suka tattauna abin da ya da ce matasa su maida hankali a kai bayan kammala babban zaben Najeriya na 2023.
Sirika ya maida martani ne kan caccakar da ya sha bayan gabatar da jirgi da ke dauke da tambarin Nigeria Air da aka gano shatar sa a ka yi daga kamfanin jirgin Ethiopia da yi masa fenti.
Akalla mutum 900 sun isa kasar mai tsarki ta Saudiya, bayan da jirgin farko da na biyu suka tashi daga filin jiragen birnin Tamale da ke Arewacin Ghanan zuwa Saudiyar.
Tun bayan ayyana cire tallafin man fetur kawunan ‘yan Najeriya ya rarrabu, yayin da wasu ke goyon baya, wasu na sukar matakin, saboda su na ganin zai shafi da dama daga cikin marasa galihu da ke fama da matsin tattalin arziki, da wasu rahotanni
Kayan masarufi da kudin sufuri sun yi tashin gauron zabi sanadiyyar janye tallafin man fetur da Shugaban kasar Najeriya Bola Tinubu ya sanar ranar da ya dauki rantsuwa, yanayin da ya sa farashin ya cira da kusan kashi 200%.
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta shirya taron sanin makamar aiki a wani bangare na shirye-shiryen kaddamar da sabuwar Majalisar ta goma da za a gudanar ranar Talata makon gobe.
Tsohon Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ana tuhumarsa da laifin karkatar da wasu takardu na sirri da aka gano a gidansa da ke Florida.
Rundunar sojin Najeriya ta ce ta damu da yadda ayyukan ‘yan ta'adda ke sake kunno kai a wasu yankuna, kuma ba za ta yarda a ci gaba da salwantar da rayukan jama'a tana kallo ba.
Hayakin da ke fitowa daga gobarar daji a kasar Canada ya kwarara har zuwa Gabashi da Yammacin tsakiyar Amurka a ranar Laraba, ya mamaye manyan biranen kasashen biyu a cikin wani yanayi mai muni.
Batun kashi talatin cikin dari na gurabun mukaman siyasa da shugabanci da mata ke nema musamman a kasashen Afrika inda aka bar su a baya, ya samo asali ne daga yarjejeniyar kasa-da-kasa da aka rattabawa hannu a birnin New York na Amurka a shekarar 1979.
Mutane akallah uku suka mutu a karamar hukumar Wukari ta jihar Taraba sakamakon rikicin kabila da ya faru tsakanin kabilun Jukun da Tiv, inda wasu da dama suka jikkata kuma yanzu haka suke asibiti ana jinyarsu.
Wasannin motsa jiki na daga cikin jerin abubuwan da suka fara jan hankulan masu bukata ta musamman a ‘yan shekarun bayan nan a kasashen Afrika
Hajjin Bana wanda ya zo da wasu sauye-sauye sakamakon rikicin Sudan da ya sanya aka rufe sararin samamniyar kasar da ya tilasta bin wasu hanyoyi tare da karawa tafiyar nisa, ka iya haifar da barazana ga lafiyar Maniyata.
‘Yan sandan Kenya sun harba barkonon tsohuwa kan daruruwan mutanen da ke zanga-zanga a kusa da majalisar dokoki a birnin Nairobi a ranar Talata, 6 ga watan Yuni.
Mobolade yayi takara ne a matsayin mai zaman kan sa, ya kuma sami nasarar kayar da wani dan jam'iyyar Republican da ya dade yana rike da mukamin bayan zagaye na biyu na zaben.
Domin Kari