Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabuwar Majalisar Dokokin Jihar Neja Ta Gayyaci Hukumomin Tsaro


Hon. Barrister Abdulmalik Mohammed
Hon. Barrister Abdulmalik Mohammed

Lamarin rashin tsaron dai ya kara ta'azzara a ‘yan kwanakin nan a jihar Nejan Najeriyar, al’amarin da ya jefa dubban mazauna yankunan karkara cikin yanayi na tashin hankali.

NIGER, NIGERIA - Dalilin da ya sa kenan sabuwar Majalisar Dokokin jihar Neja ta 10 ta gayyaci shugabannin hukumomin tsaro a jihar domin jin bahasi daga wajensu akan matsalar rashin tsaron da ke kara kamari a jihar.

Sabon shugaban Majalisar Dokokin jihar Nejan Barista Abdulmalik Sarkin Daji ya ce a ranar Laraban nan zasu gana da shugaban nin hukumomin tsaron dake aiki a jihar Neja dake zaman aiki na farko da zasu fara yi bayan kaddamar da Majalisar a ranar Talata.

A yanzu al’ummar jihar na cike da fatar ganin sabbin ‘yan majalisar za su ba da gudunmawa mai karfi da za ta taimaka wajen shawo kan matsalar tsaron a jihar.

A baya dai an sha zargin ‘yan Majalisun jihohin da zama ‘yan amshin shata ga bangaren gwamnoni bisa la’akkari da yadda suke zama tamkar rakumi da akala a tsakaninsu da banagaren zartarwar.

Amma sabon shugaban Majaliasar jihar Nejan Barista Abdulmalik Sarkin Daji ya ce a wannan karon za su hada hannu da bangaren zartarwa wajan kawo ci gaba mai amfani ga Al’umma.

A yanzu dai Al’umma na cike da fatar samun hadin kai a tsakanin bangarorin Gwamnati ta yadda za a samu nasarar shawo kan wannan matsala ta rashin tsaro da ta zama karfen kafa a wasu jihohin na Najeriya.

Saurari cikakken rahoto daga Mustapha Nasiru Batsari:

Sabuwar Majalisar Dokokin Jihar Neja Ta Gayyaci Hukumomin Tsaro.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00

XS
SM
MD
LG