Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zanga-zangar Cibok a Washington D.C


Masu zanga-zanga dake neman a nemo dalibai mata da aka sace a Cibok, sun yi dafifi a gaban Ofishin Jakadancin Najeriya dake birnin Washington D.C ran 6 ga watan Mayu, 2014.
Masu zanga-zanga dake neman a nemo dalibai mata da aka sace a Cibok, sun yi dafifi a gaban Ofishin Jakadancin Najeriya dake birnin Washington D.C ran 6 ga watan Mayu, 2014.

Gungun masu zanga-zanga ne suka taru a wajen ofishin jakadancin Najeriya a birnin Washington D.C Talatannan, suna kira a ceto dalibai mata sama da 200 da aka sace a watan da ya wuce.

An soki gwamnatin Najeriya saboda martanin tafiyar hawainiya da tayi wa lamarin, kuma kasashen duniya na kara matsa lamba akan gwamnatin a kwanakinnan.

Mutumin da yace shine shugaban kungiyar da aka fi sani da Boko Haram, yayi barazanar sayar da daliban su sama da 200 wadanda aka sace ran 14 ga watan Afrilu. Mr. Shekau yace wai Allah ne Ya ce mishi ya sayar da matan.

Masu zanga-zanga sun tura kofar shiga ofishin, suna sukar gwamnatin Najeriya saboda gazawarta na kwato daliban da wuri.

Wannan hari dai ya baiwa mutanen Najeriya mamaki saboda kamar sun sabawa da zub-da-jini tun bayan tayar da kayar da baya da ‘yan kungiyar Boko Haram suka fara a shekara ta 2009.

Masu zanga-zanga a birnin Washington sunyi kira akan a sako daliban mata, kuma suna kallonsu a matsayin “‘ya’yansu, kannensu, da ‘yan uwansu,” domin fahimtar irin hadarin da wadannan yara suka fada.

An gudanar da irin wannan zanga-zanga a birnin London, da New York kuma za’a kara yin wani a birnin na New York Larabannan. A daren jiya an sake sace yara mata masu shekaru daga 12 zuwa 15 su 8 a karamar hukumar Gwoza dake Jihar Borno. Ya zuwa yanzu gwamnatin Najeriya bata yi kalami akan wannan sabuwar sata da ta wakana ba.

Labarai masu alaka

XS
SM
MD
LG