Shugaban hukumar ta EFCC Ibrahim Lamurde ya zanta da Muryar Amurka inda ya bayyana irin matsalolin da suke fuskanta da kotu wurin yaki da cin hanci da rashawa.
Yace duk yadda za'a yi idan ba kotu ta yanke hukunci ba babu yadda jama'a zasu amince da yadda ake yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya. Abun da hukumar zata yi saidai ta kama mutum ta yi masa tambayoyi kana ta yi bincike kafin ta hada takardunta ta nufi kotu. Ba za'a tilastawa kotu ta yi abun da bata son ta yi ba.
Ya bada misali da James Ibori tsohon gwamnan Delta. Yace hukuncin dauri da aka yanke masa a Ingila kusan duk abubuwan da suka bankado aka yi anfani dasu aka daureshi. Takardun EFCC jami'an Ingila suka karba. Yace amma a nan Najeriya ga shedun ga takardun kotu tace ya tafi bashi da laifi.
To saidai bisa ga harsashe abubuwa zasu canza kwanan nan musamman a kotunan wanda zai sa da an kai kara za'a cigaba da ita kullum har sai an kare shari'ar ba tare da dageta ba kamar yadda aka saba gani..
A shari'ar da ake yi da Prince Abubakar Audu wanda yanzu yana neman gwamnan jihar Kogi an kaishi kotu a shekarar 2006 amma tun daga lokacin ko zai amsa laifin ko ba zai amsa ba nan maganar take. Banda Audu akwai Joshua Dariye da Jolly Nyame na Taraba da Uzor Kalu na Abia da Saminu Turaki na Jigawa da Farinshe na Ekiti duk wadannan shekarar 2007 aka gabatar dasu gaban kotu kuma har yau babu wanda aka kammala maganarsa.
Ga karin bayani.