Bisa ga umurnin shugaban kasa Muhammad Buhari, mai bashi shawara a harkokin tsaro ya kafa kwamiti da zai binciki yadda aka dinga sayen makamai tun daga shekarar 2007 ruwa ranar da ya karbi mulki.
An dorawa kwamitin alhakin gano kurakurai ko magudi ko karkata kudaden sayen makaman kana ya ba gwamnati shawarwari akan yadda za'a tsara sayowa jami'an tsaro makamai.
Bisa ga umurnin mai ba shugaban shawara akan harkokin tsaro ya zakulo mutanen da zasu kasance cikin kwamiti din. Wadanda aka zakulo kuwa su ne:
AVM J.O.N Ode (mai ritaya) a matsayin shugaban kwamitin. Sauran kuma su ne:
R/Admi J.A. Aikhomu (mai ritaya)
R/Admin E. Ogbor (mai ritaya)
Brig. Gen. L. Adelakun (mai ritaya)
Brig Gen M. Aminun-Kano (mai ritaya)
Brig Gen N. Rimtip (mai ritaya)
Cdre T. D. Ikoli
Air Cdre U. Mohammad (mai ritaya)
Air Cdre I. Shafi'i
Col. A. A. Aribiyi
Gp. Capt C. A. Oriaku (mai ritaya)
Mr. I.Magu (EFCC)
Brig. Gen Y. I. Shalangwa wanda shi ne sakataren kwamitin.
Kafa wannan kwamitin binciken ya zo daidai da kudurin Shugaba Buhari na kawar da cin hanci da rashawa da kuma dakile yin sama da fadi da kudaden gwamnati..
Irin kalubalen da sojojin Najeriya suka fuskanta a fafutukar da suka sha yi da 'yan ta'ada a arewa maso gabashin kasar na shekaru da dama ya sa ya zama wajibi a yi binciken. Idan ba'a manta ba an sha ikirarin bayar da makudan kudade saboda sayo makamai domin sojoji su yaki 'yan Boko Haram amma duk da hakan sojojin sun kasa tabuka wani abu saboda karancin makamai da kuma makamai da basu da inganci da rashin horon da ya kamata.. Lamarin ya karya gwiwar sojoji tare da rashin samun nasara a yakin..
Kwamitin zai mai da hankali ne musamman akan zargin cewa an ki bin ka'idodin da aka gindiya wajen sayen makamai da kuma mayar da wadanda ya kamata su ne suke da hakin sanin irin makaman da suka cancanta a saya, saniyar ware. Wasu daban ne suke yin gaban kansu su yi ruwa da tsaki wajen sayen makaman a gwamnatocin da suka shude. Hakan ya sa ana sayo makaman da basu da tasiri ko anfani ga sojojin.