Yanzu haka dai ana wasn buya tsakanin kakain majalisar dokokin jihar Ikkon Nigeria da hukumar hana cin hanci da karbar rashawa ta Nigeria, EFCC.
Hakan ko ya biyo bayan yunkurin kama Hon. Adeyemi Okoforaji kan zargin yin rub da ciki kan wasu kudi har Naira Miliyan Bakwai. Hukumar ta EFCC ta bada umarnin a kamashi duk inda aka aganshi. Wakilin sashen Hausa Ladan Ibrahim Ayawa ya tintibi ‘yan majalisar dokokin jihar Legos domin neman Karin bayani da martini, amma babu nasara. Waje daya kuma, wakilin sashen Hausa ya sami zantawa da ‘yan majalaisar dokokin jihar Jigawa da suka kai zizyarar taron karawa juna sani majalisar dokokin jihar Legos, sun kuma bayyana cewar zaman taron na kwanaki biyu zai taimaka masu kara fahimtar yadda ayyukan majalisar dokokin jihohin Nigeria ke gudana.
Saurari: