Tsohon gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ya sami belin kai lokacin hutun alkali. Alhaji Sule Lamido ya koma gida, amma ba a kai ga cika ka’idar belin ‘ya’yansa biyu ba Mustapha da Aminu wadanda ke gidan yarin Abuja dake kuje.
Mukarraban tsohon gwamnan irin su Shehu Liman na nuna cewa, EFCC bata yi masu adalci ba. Bisa ga cewarshi, bada belinshi da EFCC tayi zai iya nuna cewa, akwai wata manufa ta siyasa a ciki. Yace idan hukumar zata rika nuna danmuwa da danbora to zai nuna ke nan ba zata yiwa jama’a adalci ba. Bisa ga cewar Shehu Liman da yake gwamnati mai ci yanzu tace zata yi adalci da kuma yaki da cin hanci da rashawa, abinda ake bukatar gani shine ganin an yiwa kowa adalci.
Domin ganin nasarar aikin hukumar masu kula da lamura suka bada shawara cewa, a samar da wata kotu ta musamman da zata rika sauraron kararrakin da hukumar ta EFCC take shigarwa.
Ga cikakken rahoton da wakilinmu Nasiru Adamu el-Hikaya ya hada mana.