Wasu daga cikin mata iyayen marayu da shirin raya muradun karni na MDGs ya baiwa tallafin Naira dubu dari dari da nufin habaka tattalin arzikin su na ci gaba da kokawa game da yadda masu aiwatar da aikin a jihar Kano suka kwashe wani adadi mai yawa na kudin.
Tun a cikin shekarar da ta gabata ne hukumar ta MDGs, gabanin ta rikide ta zama SDGs, a bana ta zabe mata iyayen marayu guda dari hudu da hamsin a kowace daya daga cikin kananan hukumomi hudu da aka zabo a kananan hukumomin jahar Kano, guda arba’in da hudu da nufin basu tallafin Naira dubu dari dari kowa domin kafafa tattalin arzikin su ta yadda zasu samu sukunin kula da marayun dake gaban su kamar yadda yakamata.
Ofishin mai baiwa tsohon Gwamnan jahar Kano, shawara kan kungiyoyi da hukumomin tallafi ne ya kula da harkokin bada taimakon ga matan, amma sabanin adadin da hukumar ta MDGs, ta kayade a baiwa kowace mace.
Malama Kaltume da Hajiya Hauwa, sun bayyana korafin game da lamarin wadanda kuma suka fito daga yankin karamar hukumar Tarauni daya daga cikin kananan hukumomi hudu da suka ci gajiyar shirin.
Malama Kaltume, tace “ marayu na shida ne an bani takarda na kuma cike an kuma kirani Banki na karbi kudi Naira dubu dari a hannun masu banki, amma masu katuwar jaka sun zare dubu ashirin da biyar sun bani dubu saba’in da biyar, mun tabaya aka cema wai daga sama ne abun ba laifinsu bane.”
Yayin da matan ke korafi wasu daga cikin al’umar yankin karamar hukumar ta tarauni sun ma gabatar da wannan batu ga hukumar EFCC, domin ta bi diddigi.