A ranar Talata wata babar kotu a Abuja baban birnin taraiyar Nigeria ta bada belin Alhaji Sule Lamido tsohon gwamnan Jigawa a matsayinsa na tsohon gwamna.
An bada belin tsohon gwamnan ne tare da 'ya'yan sa guda biyu Aminu da Mustapha da kuma wani mukarabinsa Mallam Wada Abubakar.
Alkalin kotun Gabriel Kolawole ya bada belin 'ya'yan tsohon gwamnan da mukarabinsa akan kudi naira miliyan ashirin da biyar kowanensu.
Haka kuma alkali ya umarce su da su baiwa hukumomi passpo dinsu.
Hukumar EFCC ce ta kama tsohon gwamna da 'ya'yansa bisa zargin yin sama da fadi da makudan kudi, bisa zargin cewa tsohon gwamnan ya karkata akalar kudin gwamnati ko kuma na jama'a zuwa ga kamfanonisa karkashin kulawar 'ya'yansa.
Bayan da aka bada belin nasa, wakilin sashen Hausa Mahmud Kwari ya samu damar zantawa da tsohon gwamnan, inda ya nemi jin ko mai tsohon gwamnan zai fada akan fasarar kama shi da jama'a suke yi.
Alhaji Sule Lamido yace kowane dan Nigeria yana da 'yancin baiyana ra'ayinsa akan kama shi da EFCC tayi, Yace kama 'ya'yansa da aka yi yafi tada masa hankali kamar kowane uba.