A sanarwar da kakakin hukumar EFCC Mr Wilson Owojare ya fitar a Legas yace naurorin da hukumar FBI ta bayar zasu taimaka wajen binciken kwakwaf da kafa shaida a gaban kuliya a duk wasu hanyoyi da masu sace kudade ke bi wajen rufa rufa tare da batar da kudaden sata.
Binciken kwakwaf din da naurorin zasu taimaka a yi zasu sa a yiwa barayin kamun kazar kuku.
Wasu 'yan Najeriya sun bayyana ra'ayinsu akan yadda suke kallon wannan dangantaka tsakanin hukumomin biyu. Danladi Aboki mai sharhi kan harkokin yau da kullum yace FBI da Amurka kanta suna ganin dawainiya da jajircewar shugaban kasar Najeriya wurin yakar zalunci da azzalumai. Manufar shugaban Najeriya ita ce a rabu da sace-sace dalili ke nan da ya sa Amurka ta tashi ta yi taimako.
Karamar jakadiyar Amurka dake Abuja ce ta mika naurar ga mataimakin hukumar EFCC Iliyasu Kwarbai tare da yabawa da aikin hukumar wajen magance matsalolin cin hanci da rashawa da kuma yiwa tattalin arzikin zagon kasa.
To saidai duk da yabon da hukumar EFCC ta samu, a cewar shugaban hukumar Malam Ibrahim Lamurde akwai bukatar yin gyara ga kundun tsarin mulkin kasa saboda hukumar ta samu hukumta masu laifi cikin hanzari ba tare da jeka ka dawo da ake fuskanta a kotunan kasar ba.
A cewar Barrister Idris Doko dake Legas yace idan kai yayi kyau dole gangar jiki ta yi kyau. Kasar nada dokokin da zasu hukumta duk wanda ya yi laifi idan babu wani shugaba da zai hana a yi hukumci. Kuma idan shi shugaban kasa baya cin hanci ko wawurar dukiyar jama'a da wuya wasu su yi gaba gadi.
Ga rahoton Babangida Jibrin.