WASHINGTON, DC —
Wakilan majalisar dokokin Jihar Kano, wacce gwamnanta da mukarrabansa suka chanja shekarar siyasarsu daga jam’iyyar PDP mai mulkin Nigeria zuwa sabuwar jam’iyyar adawa ta APC, sun sami “gayattar” musamman daga wajen Hukumar hana wanzuwar aiyukkan mundahana ta Nigeria, watau EFCC, don, a cewarta, su taimaka mata a binciken da take gudanarwa a Kano. Sai dai kuma wasu na ganin cewa wannan kamar “bi ta da kulli” ne ake wa jihar saboda sauya shekar siyasar da tayi. Daga Kanon, ga rahoton da wakilinmu Mahmud Ibrahim Kwari ya aiko mana:
Hukumar EFCC ta kiranyo manyan jagabannin majalisar dokokin Kano