Duk da fadakarwa da magabata suka yi wa ‘yan siyasa a Najeriya har yanzu ana samun munanan kalamai da ke iya tunzura jama'a da tayar da fitina a lokutan zabubbuka.
Wasu ‘yan takarar kujerar gwamna sun bayyana ra'ayoyinsu game da dage ranar zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi, daga ranar Asabar 11 ga watan Maris zuwa ranar 18 ga watan.
Hukumar zaben Najeriya ta INEC ta dage gudanar da zaben gwamnoni da 'yan majalisar jiha zuwa ranar Asabar 18 ga watan Maris.
Babbar kotun tarayya dake Kano ta bada belin shugaban masu rinjaye na Majalisar Wakilan Najeriya, Alhassan Ado Doguwa, wanda ke fuskantar tuhumar kisan kai da rike makami ko mallakar makami babu izinin hukuma.
Tawagar dan takarar jam’iyyar PDP a babban zaben 2023 Atiku Abubakar, ta gudanar da zanga-zangar lumana zuwa hukumar zabe don nuna rashin amincewa da sakamakon zaben.
Rundunar 'yan sanda a jihar Kano ta ce ta bankado wani yunkuri da wasu batagarin ‘yan siyasa ke yi na shiga da makamai cikin jihar, domin amfani da su a yayin zaben gwamna da na ‘yan majalisar dokokin jihohi da za’a yi ranar Asabar mai zuwa
Kungiyar kiristocin Najeriya (CAN) reshen matasa a arewacin kasar ta bukaci duk mabiya su kwantar da hankalin su biyo bayan ayyana Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa a Najeriya.
Kotun daukaka kara ta bai wa dan takarar jam'iyyar PDP Atiku Abubakar da na jam'iyyar Labour Peter Obi hurumin hukumar zabe ta ba su dama su binciki kayan da a ka yi amfani da su wajen gudanar da babban zaben 2023.
A Najeriya, Jamiyyun adawa uku wadanda aka yi zaben Shugaban Kasa tare da su, a ranar asabar 25 ga watan Fabrairu na wanan shekarar, sun bayyana matakan da za su dauka bayan da hukumar zabe ta kasa ta ayyana dan takarar Jamiyyar APC mai mulki a matsayin wanda ya lashe zaben.
Hukumar zabe ta INEC ta ce duk wanda bai gamsu da sakamakon zaben ba zai iya gabatar da korafinsa a gaban kotu.
Obi ya ce za su bi duk wata hanya da doka ta tanada domin ganin sun kwato hakkinsu.
Domin Kari