Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Tarayya Ta Bada Belin Alhassan Doguwa


Alhassan Ado Doguwa
Alhassan Ado Doguwa

Babbar kotun tarayya dake Kano ta bada belin shugaban masu rinjaye na Majalisar Wakilan Najeriya, Alhassan Ado Doguwa, wanda ke fuskantar tuhumar kisan kai da rike makami ko mallakar makami babu izinin hukuma.

Kotun Majistire ta Kano karkashin jagorancin mai shari’a Ibrahim Mansur Yola, ita ce ta mika Alhassan Ado Doguwa zuwa gida ajiya da gyaran hali a ranar alhamis da ta gabata, bayan da ‘yan sanda suka gurfanar dashi, suna tuhumar sa da hannu a tarzomar zabe da ta wakana a garin Tudunwada na yankin kudancin Kano, inda a kalla mutane uku suka mutu wasu da dama suka jikkata lokacin da magoya bayan Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya da na NNPP mai hamayya suka yi arangama da juna a wurin tattara sakamakon zabe a yankin.

Sai dai alkalin kotun tarayya mai shari’a Muhammad Nasir Yunus, ya bada belin Alhassan Ado Doguwa, yana mai cewa, kotun majistire ta mai shari’a Ibrahim Mansur ba ta da hurumin sauraron shari’ar kuma ci gaba da tsare wanda ake tuhuma tauye ‘yancin sa ne na dan kasa.

Mai shari’a Muhammad Yunus, ya gidaya sharadin belin Alhassan Ado da cewa, sai sarkin Yanka mai daraja ta daya da kuma babban ma’aikacin gwamnati a matakin tarayya ko jiha sun tsaya masa, kana tilas ne ya mika fasfo din sa na tafiye tafiye ga zauren kotun kuma wajibi ne masu tsaya masa beli, su biya naira miliyan dari biyar muddin ya ki bayyana a lokacin da kotu ta neme shi.

Kazalika, kotun ta haramtawa Alhassan Ado Doguwa ziyartar yankin mazabar sa a yayin zaben gwamnoni da za’a yi a Najeriya, ranar asabar mai zuwa 11 ga wannan wata na Maris.

Wakilinmu a Kano Mahmud Ibrahim Kwari ya ruwaito cewa, da-ma a gobe talata ne ake sa ran shirya cajin tuhuma da za’a gurfanar da Alhassan Ado a gaban babbar kotu, bayan da ma’aikatar shari’a ta jihar Kano ta kammala wallafa kudin tuhume-tuhume akan sa.

XS
SM
MD
LG