Tawagar bisa jagorancin wasu shugabannin jam’iyyar PDP da shi kansa Atiku Abubakar sun bukaci a soke sakamakon zaben da aka gudanar fadin kasar.
Zanga-zangar da a ka dade ba a ga irin ta ba, zuwa hukumar Zaben na zuwa ne bayan kotun daukaka kara ta ba da hurumi ga dan takarar na PDP Atiku da na Leba Obi, su duba kayan da a ka yi amfani da su wajen zaben musamman na’urar BVAS da ‘yan adawar su ka ce sam ba a yi amfani da ita ba.
Kakakin kamfen din Atiku, Dino Melaye, ya ce sam ba za su amince da sakamakon ba kuma sun nuna hakan a lokacin da su ka fice daga dakin bayyana sakamakon gabanin kammala kawo sakamakon zaben.
Tawagar ta mika wasika da ke kunshe da dukkan korafe-korafen ‘yan adawar, inda kwamishina mai kula da wayar da kan masu kada kuri’a Festus Okoye, ya karba ya yi alwashin mikawa shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu.
“Hukumar nan ba ta daukar umurni daga wajen kowace jam’iyyar siyasa, aikin ta ga ‘yan Najeriya ne, za mu dau mataki kan sashen wasikar da ya shafi shari’a kuma za mu duba dukkan abun da a ka rubuta” a cewar Okoye.
In za a tuna bayan zaben 2011 gabanin zaben 2015, shugaba Buhari ya jagoranci irin wannan zanga-zanga zuwa hukumar zaben da samun rakiyar shugabannin APC karkashin John Odigie Oyegun.
Buhari a lokacin ya nuna takaicin zaben 2011 da togaciyar lalle a samu sauyi a 2015 inda kuma cikin ikon Allah ya samu nasara.
Domin karin bayani saurari rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya: