A Najeriya, Jamiyyun adawa uku wadanda aka yi zaben Shugaban Kasa tare da su, a ranar asabar 25 ga watan Fabrairu na wanan shekarar, sun bayyana matakan da za su dauka bayan da hukumar zabe ta kasa ta ayyana dan takarar Jamiyyar APC mai mulki a matsayin wanda ya lashe zaben.
Hukumar zabe ta INEC ta ce duk wanda bai gamsu da sakamakon zaben ba zai iya gabatar da korafinsa a gaban kotu.
Obi ya ce za su bi duk wata hanya da doka ta tanada domin ganin sun kwato hakkinsu.
Shugaban hukumar zaben Najeriya INEC Farfesa Mahmood Yakubu ta mika shaidar lashe zabe ga zababben shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu.
'Yan takarar shugaban kasa na jam'iyyar adawa a Najeriya sun ce za su kalubalanci sakamakon zaben da ya ayyana dan takarar jam'iyya mai mulki a matsayin wanda ya yi nasara.
Manyan jam’iyyun siyasar kasar na bangaren ‘yan adawa ciki har da LP, sun nemi a yi watsi da sakamakon zaben, suna masu ikirarin an tafka magudi, ikirarin da INEC ta musanta.
Da asubahin yau Laraba ne hukumar zaben Najeriya ta ayyana dan takarar jam'iyyar mai mulki ta APC, Bola Tinubu a matsayin zababben shugaban kasa, bayan da aka gudanar da zaben a karshen mako cike da takaddama, yayin da manyan jam'iyyun adawa biyu suka yi watsi da sakamakon.
Hukumar Zabe mai zaman kanta a Najeriya ta bayyana Bola Tinubu na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka yi a ranar Asabar 25 ga watan Fabrairu.
Jam’iyyar New Nigerian Peoples Party (NNPP) ta bi sahun jam’iyyun PDP da na LP wajen kiran da a soke zaben shugaban kasa da na majalisun dokoki da a ka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.
A ranar Litinin wasu daga cikin wakilan jam'iyyun na bangaren 'yan adawa suka fice daga zauren tattara sakamakon zaben bayan da suka nuna rashin gamsuwar kan abin da ke faruwa.
Yayin da wasu wakilan jam’iyyun adawa su ka marawa PDP da Leba wajen ficewa daga dakin tattara sakamakon zaben shugaban Najeriya, wasu bangaren na ‘yan adawa sun kara gyara zama ne da nuna sun yi na’am da yanda sakamakon ke fitowa.
Domin Kari