Hakan na zuwa ne a dai-dai lokacin da gamayyar ‘yan takarar gwamna na jam’iyyun hamayya, banda NNPP suke cewa jihar ta Kano na fuskantar barazanar tsaro a wannan zabe da ke tafe.
A taron manema labarai da aka yi a birnin Kano, ‘yan takarar jam’iyyun na ADC da ADP da PDP da NRM da kuma YPP sun yi Allah wadai da yunkurin da suka ce wasu batagarin ‘yan siyasa a jihar na yi don kawo tarzoma da za ta haifar da cikas ga tafarkin gudanar da sahihin zabe.
Malam Ibrahim Khalil, dan takarar Jam’iyyar ADC gwamnan Kano, a zaben na ranar Asabar mai zuwa shine ya karanta sakon a madadin sauran takwarorin sa a yayin ganawar da suka yi da manema labarai.
Ya bukaci hukumomi tsaro da masu sanya idanu akan harkokin zabe na ciki da wajen Najeriya, da sauran masu ruwa da tsaki akan al’amuran zabe su dauki matakan da suka dace don tabbatar da cewa an yi zaben cikin lumana.
A hannu guda kuma, ita ma rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ta fitar da wata sanarwa, dake nuna cewa za ta sanya kafar wando guda da dukkanin wani dan siyasa dake yunkurin tada zaune tsaye a jihar ta Kano.
Rundunar ta cikin sanarwa da kakakin ta SP Abdullahi Kiwaya ya fitar, ta ce rahottanin sirri na nuni da cewa, wasu miyagun ‘yan siyasa na takidin amfani da batagarin matasa domin tada tarzoma a jihar ta Kano, a yayin zaben ranar Asabar mai zuwa. Sai dai ta ce za ta yi aiki kafada da kafada da sauran hukumomin tsaro wajen murkushe yunkuri irin wannan.
Yanzu haka dai masana harkokin tsaro sun fara tsokaci akan wannan batu.
Masanin harkokin tsaro Auwalu Bala Durumin Iya, mai sharhi ne akan lamuran tsaro a Najeriya, ya ce muddin hukumomin tsaro ba su dauki matakan da suka dace ba, babu shakka akwai yuwuwar Kano ta fuskanci shiga yanayi na tarzoma da ka iya haifar da hasarar rayuka da dukiya.
A makon jiya ne dai rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ta gurfanar da shugaban masu rinjaye a Majalisar Wakilan Najeriya, a gaban kotu bisa zargin sa da hannu cikin tarzomar zabe, yayin da shi-ma zababben dan Majalisar tarayya a Jam’iyyar NNPP ya amsa gayyatar rundunar dangane da tuhumarsa kan zargin mallakar bindiga babu izini.
Domin karin bayani saurari rahotan Mahmud Ibrahim Kwari: