Tsohon mataimakin Shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, yayi martani ga hukuncin da kotun koli ta yanke na baya-bayan nan, tare da yin kakkausar suka dangane da tasirin hukuncin da kotun ta yanke a zaben 2023.
A yau Litinin aka rantsar da Bola Tinubu a matsayin shugaban kasar Najeriya, bayan da aka gudanar da zaben cike gurbi da kuma fuskantar matsin lamba kan ya gaggauta inganta yanayin tattalin arziki da tsaro.
Bayan rantsar dashi a 29 ga Mayu, Ahmed Bola Tinubu na zaman shugaban Najeriya na 16, a daidai lokacin da yawan ‘yan kasar ya zarta miliyan 200.
A zaman da ta yi ranar Laraba 10 ga watan Mayu, kotun sauraron kararrakin kalubalantar nasarar da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC Bola Ahmed Tinubu ya samu a zaben 2023 ta yi watsi da karar da jam’iyyar APP ta shigar bayan da lauyan da ke kareta ya ce sun janye karar.
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce ta sami nasarar cafke kwamishinan hukumar zaben ta kasa INEC na Jihar Adamawa, Hudu Ari, wanda ya yi riga-malam masallaci wajen ayyana sakamakon zaben gwamnan jihar Adamawa tun ba'a kammala tattara sakamakon baki daya ba.
Sai dai gwamnan na Adamawa bai kama sunan wadanda yake ikirarin da su ya yi takarar ba.
Majalisar Darektocin Jam'iyar PDP sun ja hankalin Hukumar Zaben Najeriya ta kiyaye sauya sakamakon zaben jihar Adamawa bayan riga-mallam massalacin da wani jami'in Hukumar zabe ya yi
Jami’in tattara sakamakon zabe ya ayyana Idris a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kebbi ranar Lahadi 16 ga watan Afirilu.
An girke jami'an tsaro masu yawa yayin da jama’a suka nufi rumfunan zaɓe ranar Asabar don a kaɗa ƙuri'ar zaɓen gwamna a Yola babban birnin Jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya.
A farkon makon nan hukumar INEC ta ayyana dan takarar NNPP, Abba Kabir Yusuf, wanda aka fi sani da Abba Gida-gida, a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamna a jihar, wanda aka yi a ranar 18 ga watan Maris a Najeriya.
A ranar Talata ne jagororin manyan jami’iyyun adawa a Najeriya biyu suka shigar da kara a kan neman soke sakamakon zaben shugaban kasa na watan Fabrairu da suke kalubalanta, kamar yadda takardun kotu su ka nuna, domin fara wata shari’ar da ka iya daukar tsawon watanni.
Domin Kari