Dan takarar kujerar gwamna a jihar Sokoto a karkashin jam’iyyar SDP Sanata Abubakar Umar Gada, ya ce dage ranar zaben da hukumar INEC ta yi bai zo masa da mamaki ba, domin akwai wasu kalubale da hukumar ke fuskanta, musamman idan aka yi la'akari da cece-ku-ce da takaddama da ke tsakani hukumar zaben da ‘yan takara na zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya.
Gada ya ce tuni aka garzaya kotu saboda neman bahasi kan al'amarin, a saboda haka yana ganin wannan ya janyo ayar tambaya da zata sa ba za a iya aiki da na'urar BVAS ba sai an gama bincike akanta, kamar yadda masu kai kara suka nema.
Gada ya kara da cewa fatan sa shi ne hukumar zabe ta samu ta kammala aikin cikin lokaci saboda kada a takura wa wadanda za su yi zaben, kuma yana fatan hakan shi ne mafi alheri a garesu.
Shi kuwa dan takarar kujerar gwamna a karkashin jam’iyar NNPP mai kayan marmari a jihar Bauchi, Sanata Haliru Jika, yana mai cewa dage ranar zaben da INEC ta yi bai daga masa hankali ba, domin yana da karfin gwiwa shi zai ci zabe a jihar Bauchi. Jika ya kuma yi fatan jinkirin zai zama alheri.
Hukumar zaben dai ta nemi sake fasalin tsarin tantance na'urar masu kada kuri'a ta BVAS, kamar yadda kotun daukaka kara ta amince a jiya Laraba.
Saurari cikakken rahoton Medina Dauda: