Kungiyoyin mata sama da 500 ne suka hadu a karkashin kungiyar Womanifesto a Abuja don jan hankalin masu neman takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2023, da su tabbata sun bada fifiko kan batutuwan da suka shafi mata a cikin manufofinsu, in ba haka ba zasu kauracewa zaben gaba daya.
Gabanin zaben shekarar 2023 a Najeriya, masu ruwa da tsaki a Jihar Kano sun gudanar da wani gangamin wayar da kan ‘yan bangar siyasa da nufin ganin ba a yi amfani da matasan yankin wajen tayar da rikici a lokacin zabe ba.
Magoya bayan ‘yan takarar shugabancin Najeriya na nuna yanda gwanayensu su ka yi zarra kan juna, yayin da kamfen din zaben 2023 ya fara kankama.
Taron yakin neman zaben ‘dan takarar shugaban kasa na Jam'iyyar PDP a Jihar Kaduna ya yi karo da tasgaro biyo bayan afka wa taron da wasu matasa dauke da makamai su ka yi inda su ka jikkata wasu mahalarta taron, to sai dai kuma wannan bai hana taron ba.
Jam’iyyar APC mai mulikin Najeriya ta sanar da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC cewa Bashir Machina shine dan takararta na Sanatan Yobe ta Arewa, matakin da a karshe ya tabbatar da makomar takarar shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan.
Mahmud Yakubu wanda ke magana a wata ziyara a Amurka a taron da asusun raya dimokradiyya da kuma asusun tallafawa tsarin zabe na duniya su ka shirya, ya ce labarun karya ya zama kalubale da ke kawo damuwa kan babban zaben Najeriya.
“Karrama Gwamna Ifeanyi A. Okowa da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi, manuniya ce cewa na zabi mutum na gari a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa a zaben 2023. In ji Atiku.
Manazarta a fagen siyasar Najeriya da ke sharhi kan harkokin dimokradiyyar kasar, sun fara bayyana mabanbantan ra’ayi dangane da kamun ludayin laffuzan ‘yan takara bayan bude labulen fara kamfe da hukumar zabe ta yi na tunkarar babban zaben 2023.
Yayin da harkokin siyasa suka kankama gadan-gadan a Najeriya, wasu ‘yan kasar na mamakin yadda gwamnatocin siyasa da suka yi mulki suka kasa warware matsalolin rayuwa ga jama'a, tare da nuna fargabar kada gwamnati mai zuwa ta bi sawun ta baya.
Jiga-jigan ‘ya’yan babbar jam’iyar adawa ta PDP daga sassan Najeriya karkashin jagorancin shugaban jam’iyar ta kasa, Dr. Iyorchia Ayu, sun kai ziyarar marabtar wasu ‘yan siyasa sama dubu 140 da suka sauya sheka zuwa jam’iyyar ta PDP.
A wasu jihohin kamar Lagos an samu kimanin ‘yan takara 15 na gwamna daga jam’iyyu daban-daban ciki har da APC mai mulki da babbar jam’iyyar adawa ta PDP.
An yi ta ce-ce-ku-ce kan halin da Tinubu yake ciki bayan da ya gaza halartar taron kulla yarjejeniyar zaman lafiya da aka yi a tsakanin jam’iyyun siyasar kasar a makon da ya gabata a Abuja.
Domin Kari