Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN 2023: Machina Ya Tabbata Dan Takarar Sanatan APC A Yobe Ta Arewa


Bashir Machina/Ahmed Lawan
Bashir Machina/Ahmed Lawan

Jam’iyyar APC mai mulikin Najeriya ta sanar da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC cewa Bashir Machina shine dan takararta na Sanatan Yobe ta Arewa, matakin da a karshe ya tabbatar da makomar takarar shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan.

A wata wasika da aka rubuta ranar 12 ga watan Oktoba mai dauke da sa hannun Shugaban jam’iyyar Abdullahi Adamu da sakataran jam’iyyar Iyiola Omisore, jam’iyyar APC ta bukaci ofishin hukumar zaben da ya buga sunan Bashir Machina a matsayin dan takarar jam’iyar kamar yadda hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ke Damaturu ya umarta a ranar 28 ga watan Satumba.

Kotun ta tabbatar da Machina a matsayin dan takarar jam’iyyar APC da aka zaba a zaben fidda gwani na jam’iyyar a ranar 28 ga watan Mayu. Lawal ya yi kokarin yin amfani da damarsa ta siyasa da kudi da yake da shi wajen kwace tikitin takarar daga Machina.

Shugaban Majalisar Dattawan bai shiga zaben fidda gwani na ‘yan majalisar dattawa ba saboda ya shiga zaben fidda gwani na shugaban kasa a Abuja, wanda ya sha kaye a hannun Tinubu, da aka tsayar a matsayin dan takarar jam’iyyar na shugaban kasa a zaben 2023.

Bin umarnin kotun tarayya da jam’iyyar APC ta yi na tabbatar da cewa, Lawan ba zai sake komawa majalisar dattawa ba tun lokacin da aka zabe shi karon farko a shekarar 1999.

An sanya ido sosai a kan shari’ar a duk fadin kasar a matsayin gwaji a jajircewar jam’iyyar APC na tabbatar da tsarin dimokaradiyya na cikin gida da kuma ‘yancin kai na hukumar INEC a matsayinta mai sasantawa kuma mai kula da tsarin zaben kasa.

XS
SM
MD
LG