Jiga-jigan ‘ya’yan babbar jam’iyar adawa ta PDP daga sassan Najeriya karkashin jagorancin shugaban jam’iyar ta kasa, Dr. Iyorchia Ayu, sun kai ziyarar marabtar wasu ‘yan siyasa sama dubu 140 da suka sauya sheka zuwa jam’iyyar ta PDP.
A wasu jihohin kamar Lagos an samu kimanin ‘yan takara 15 na gwamna daga jam’iyyu daban-daban ciki har da APC mai mulki da babbar jam’iyyar adawa ta PDP.
An yi ta ce-ce-ku-ce kan halin da Tinubu yake ciki bayan da ya gaza halartar taron kulla yarjejeniyar zaman lafiya da aka yi a tsakanin jam’iyyun siyasar kasar a makon da ya gabata a Abuja.
Batun kiyaye laffuza da kalamai yayin tallar ‘yan takara na daga cikin muhimman abubuwan da suka mamaye jawaban shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na cikar kasar shekaru 62 da samun ‘yanci daga Turawan mulkin mallaka na kasar Burtaniya.
Cikin wannan hirar da Muryar Amurka ta yi da tsohon shugaban Najeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya tabo batutuwan da suka shafi zaman lafiya, zaben 2023 tare da yin kira ga matasa kan kada su bari a yi amfani da su don zarafin wani a siyasa.
Shugaban majalisar dattawan Najeriya Ahmad Lawal ya amince da Bashir Machina a matsayin dan takarar jam’iyyar APC a zaben Sanatan Yobe ta Arewa a shekarar 2023.
Duk da bude damar fara yakin neman zabe da hukumar zaben Najeriya ta INEC ta yi, ‘yan takarar manyan jam’iyyu da ke alwashin shiryawa tsaf don tinkarar zaben 2023 ba su kaddamar da kamfe ba.
Ranar Larabar nan aka kaddamar da fara kamfen din ‘yan takarar shugaban kasa na babban zaben Najeriya da za a gudanar a watan Febrairun 2023.
A yau Laraba 28 ga watan Satumba aka fara yakin neman zaben 2023 a hukumance a Najeriya.
Rundunar sojojin Najeriya ta ja kunnen masu rura wutar rikici a sassa daban daban na kasar da su yiwa kansu kiyamullayli, domin kuwa rundunar zata dau duk wani matakin da ya dace kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya bata wajen ganin ta kare yan kasa na gari.
“Yanzu haka muna shirin gudanar da zabe a watan Fabrairu mai zuwa, taron Majalisar Dinkin Duniya da za a yi (badi) a karo na 78, bakuwar fuska za ku gani a nan yana magana da yawun Najeriya.” In ji Buhari.
Alamu na nuna babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta yi matsayar hakura da rarrashin gwamnan Ribas Nyesom Wike da ke cewa lalle sai shugaban jam’iyyar Iyorchia Ayu ya sauka daga mulki don kujerar ta koma kudancin kasar.
Domin Kari