Jam’iyyar All Progressives Party (APC) mai mulki a Najeriya, ta yi karin haske game da dalilin da ya sa dan takarar mukamin shugaban kasa karkashin jam’iyyar Bola Ahmed Tinubu ya tafi birnin London.
Rahotannin baya-bayan nan sun yi ta nuna ba a san inda Tinubu yake ba, lamarin da ya sa wasu suka fara tunanin rashin ganinsa da ba a yi na da nasaba da lafiyarsa.
Sai dai yayin wata hira da ya yi da gidan talabijin na Channels, daya daga cikin mambobin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa a jam’iyyar ta APC, Ayo Oyalowo, ya ce, Tinubu ya je London ne don ya kimtsawa yakin neman zabe.
“Tinubu na bukatar ya dauki hutun wasu ‘yan kwanaki saboda abubuwa sun masa yawa, yana kuma bukatar ya huta saboda yakin neman zabe da aka shiga zai kasance mai tsayi.” Oyalowo ya fada a shirin Politics Today a ranar Litinin.
Gabanin kalaman na Oyalowo, Tinubu da kansa ya wallafa a shafukan sada zumunta cewa yana nan cikin koshin lafiya.
“Mutane da dama sun ce na mutu; wasu kuma sun ce na janye daga yakin neman zaben shugaban kasa……. ba haka ba ne.
“Gaskiyar magana ita ce, ina cikin koshin lafiya kuma a SHIRYE nake na fara yi wa ‘yan Najeriya hidima daga ranar farko.” Tinubu ya ce a shafinsa na Facebook inda ya hada sakon da wani hoton bidiyo da ya nuna shi yana motsa jiki.
An yi ta ce-ce-ku-ce kan halin da Tinubu yake ciki bayan da ya gaza halartar taron kulla yarjejeniyar zaman lafiya da aka yi a tsakanin jam’iyyun siyasar kasar a makon da ya gabata a Abuja.
Kazalika bai halarci babban taron da kungiyar lauyoyin Najeriya ta shirya a Legas a watan Agusta ba.
Sai dai ya tura abokin takararsa Kashim Shettima don wakilce shi a dukkan tarukan.
A ranar 28 ga watan Satumba aka fara yakin neman zabe a hukumance, za kuma a yi zaben shugaban kasa a watan Fabrairun badi.