Shugaban majalisar dattawan Najeriya Ahmad Lawal ya amince da Bashir Machina a matsayin dan takarar jam’iyyar APC a zaben Sanatan Yobe ta Arewa a shekarar 2023.
Duk da bude damar fara yakin neman zabe da hukumar zaben Najeriya ta INEC ta yi, ‘yan takarar manyan jam’iyyu da ke alwashin shiryawa tsaf don tinkarar zaben 2023 ba su kaddamar da kamfe ba.
Ranar Larabar nan aka kaddamar da fara kamfen din ‘yan takarar shugaban kasa na babban zaben Najeriya da za a gudanar a watan Febrairun 2023.
A yau Laraba 28 ga watan Satumba aka fara yakin neman zaben 2023 a hukumance a Najeriya.
Rundunar sojojin Najeriya ta ja kunnen masu rura wutar rikici a sassa daban daban na kasar da su yiwa kansu kiyamullayli, domin kuwa rundunar zata dau duk wani matakin da ya dace kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya bata wajen ganin ta kare yan kasa na gari.
“Yanzu haka muna shirin gudanar da zabe a watan Fabrairu mai zuwa, taron Majalisar Dinkin Duniya da za a yi (badi) a karo na 78, bakuwar fuska za ku gani a nan yana magana da yawun Najeriya.” In ji Buhari.
Alamu na nuna babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta yi matsayar hakura da rarrashin gwamnan Ribas Nyesom Wike da ke cewa lalle sai shugaban jam’iyyar Iyorchia Ayu ya sauka daga mulki don kujerar ta koma kudancin kasar.
"Jam’iyyar PDP na kira ga gwamnatin jihar Gombe da ta yi maza-maza ta sake gina mana ofishin kamfen dinmu tare da neman afuwar al’umar jihar." PDP ta ce.
Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa a Najeriya Farfesa Mahmood Yakubu ya ce hukumar ta na ci gaba da shirye-shirye na musamman don ganin 'yan gudun hijara sun kada kuri’a a zaben 2023.
Shugaban kwamitin amintattu na jam'iyyar PDP a Najeriya wanda ya yi murabus ya ce ya ajiye mukamin sa ne don samun sulhu a jam’iyyar, bisa korafin yawan mukamai a yankin arewacin kasar.
A kwanakin baya, rahotanni sun yi nuni da cewa Walid Jibrin da kansa ya fito ya ce bai dace a ce dan takarar shugaban kasa da shugaban jam’iyya su fito daga yanki daya ba.
Yayin da jam’iyyar APC mai mulki ke kokarin ganin ta ci gaba da zama a kan karagar mulki, ita kuwa PDP kokari take ta ga mulkin ya dawo hannunta.
Domin Kari