Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Lambar Girma Da Buhari Ya Ba Okowa, Shaida Ce Ban Yi Zaben Tumun Dare Ba – Atiku 


Lokacin da Buhari ya karrama Okowa da lambar girmamawa (Facebook/Atiku Abubakar)
Lokacin da Buhari ya karrama Okowa da lambar girmamawa (Facebook/Atiku Abubakar)

“Karrama Gwamna Ifeanyi A. Okowa da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi, manuniya ce cewa na zabi mutum na gari a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa a zaben 2023. In ji Atiku.

Dan takarar shugaban kasa karkashin babbar jam’iyyar adawa ta Peoples’ Democratic Party (PDP)Atiku Abubakar, ya ce lambar girma da shugaba Muhammadu Buhari ya ba gwamnan jihar Delta Ifeanyi Okowa, alama ce da ke nuna cewa bai yi zabin tumun dare ba.

A ranar Talata shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya karrama ‘yan Najeriya da wasu ‘yan kasashen waje 447 da lambobin giramamawa a wani kasaitaccen taro da aka yi a Abuja, babban birnin kasar.

“Karrama Gwamna Ifeanyi A. Okowa da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi, manuniya ce cewa na zabi mutum na gari a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa a zaben 2023.

“A madadin iyalina, tawagata da magoya bayana, muna taya ka murna.” Atiku ya ce cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Talata.

XS
SM
MD
LG