Kasa da sa'o'i 24 bayan da kafofin yada labaran Amurka suka yi hasashen cewa tsohon mataimakin Shugaban Amurka Joe Biden ne ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi ranar 3 ga watan Nuwamba, duk da cewa Shugaban Amurka Donald Trump bai amince da sakamakon zaben ba, ‘yan Najeriya sun bi sahun sauran kasashen duniya wajen bayyana ra'ayoyinsu da kuma yi wa Amurka fatan alheri.
Wani masanin harkokin tattalin arziki da hannayen jari, Dr. Dauda Muhammed Kwantagora, ya ce Najeriya na daga cikin manyan kawayen huldar Amurka a Afrika kuma duk da sabuwar gwamnatin da za a kafa dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu ba za ta canza ba.
Wasu mazauna birnin Legas sun ce, suna ganin ta yiwu nasarar da Biden ya samu za ta kara inganta dangantaka tsakanin Amurka da kasashen duniya. Wasu kuma sun yi fatan Biden zai kawo hadin kai tsakanin al'ummar Amurka da ma sauran kasahen duniya.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na daga cikin shugabannin duniya da suka taya Joe Biden murnar samun nasara a zaben.
Ga karin bayani a cikin sauti daga Babangida Jibrin.
Facebook Forum