Akalla Falasdinawa 104 ne aka kashe a birnin Gaza ranar Alhamis yayin da sojojin Isra’ila suka bude wuta kan mutanen da ke kokarin samun abinci daga manyan motocin jin kai.
Shugaban Amurka Joe Biden da tsohon shugaban kasar Donald Trump sun lashe zaben fidda gwani na jam'iyyarsu a jihar Michigan ranar Talata.
Makarantar koyon aikin likita a birnin New York za ta zama kyauta ga duk ɗalibai daga yanzu saboda gudummawar dala biliyan 1 daga wata tsohuwar farfesa, gwauruwar wani mai saka hannun jari na Berkshire Hathaway.
Shugaban Amurka Joe Biden da tsohon shugaban kasar Donald Trump za su nufi kan iyakar Amurka da Mexico a cikin wannan mako, inda za su maida hankali kan daukar matakan gaggawa dangane da cigaba da kwararar dubun dubatan bakin haure da ke ke shigowa Amurka.
Firai Ministan Isra'ila ya fada a ranar Lahadi cewa, yuwuwar tsagaita wuta a yakin da kasarsa ke yi da mayakan Hamas zai jinkirta kai hari ta kasa ne kawai a birnin Rafah da ke kudancin Gaza, inda ya zama mafaka ga fiye da rabin al'ummar yankin da ke fuskantar rikici.
Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi a ranar Litinin cewa, rashin abinci mai gina jiki, da kuma yaduwar cututtuka na iya haifar da kazamin mutuwar yara a Gaza.
Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Linda Thomas-Greenfield, ta ce Amurka ba za ta goyi bayan kudurin ba a yadda aka tsara shi.
A wani hukuncin da ake ganin ya na iya lahani ga harkokin kasuwancin tsohon Shugaban Amurka, Donald Trump, an ci shi tarar kudi mai yawa a birnin New York baya ga takunkumin kasuwanci da aka kakaba ma shi.
Robert DuBoise ya shafe shekaru 37 a gidan yarin Florida saboda laifin fyade da kisan kai a 1983 da bai aikata ba. Yanzu jihar Florida za ta biya shi dala miliyan 14 a matsayin diyya na tsawon shekarun da yake daure.
Wata mata mai ‘ya’ya biyu ta mutu sanan mutane 21, ciki har da akalla yara takwas, sun raunata a yayin wani harin bindiga da ya auku a wani tashar jirgin kasa mai tarihi da ke birnin na Kansas a Jihar Missouri.
A jiya laraba Amurka ta dorawa wasu mutane 3 da kamfanoni 4 takunkumi a sassan kasashen Iran, da hadaddiyar daular larabawa da Turkiyya, bisa dalilin zargin su da taimakawa wajen fitar da kayayyaki, da sayen fasahohi daga kamfanonin Amurka zuwa kasar Iran da babban bankin kasar.
An sake kama wani mutum da ake nema ruwa a jallo a jihar Massachusetts domin fuskantar tuhumar kisan kai, mako guda bayan ya tsere da dubara daga hannun ‘yan sanda, in ji ‘yan sandan Kenya a ranar Laraba.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.