Mataimakiyar sakatarin al’adu da ilimi a ma’aikatar harkokin wajen kasar Amurka, Lee Satterfield, ta bayyana haka ne a jami’ar Legas a ranar Laraba inda ta bayyana manufofin kasashen waje kan sabbin shirye-shiryen.
Zaman dardar ya karu yayin da shugaban Hamas ya zargi Isra'ila a ranar Talata da yin zagon kasa ga tattaunawar ake yi ta tsagaita bude wuta a Gaza bayan da, a karo na biyu, Isra’ilar ta kai farmaki a asibiti mafi girma a yankin Falasdinu da ya daidaice.
A yau Litinin Donald Trump ya gaza samun takardar shaidar da za ta ba shi damar daukaka kara kan hukuncin dala miliyan 454 da aka yanke wa tsohon shugaban na Amurka a wani zambar a birnin New York ba tare da damar tura kudin da kansa ba, a cewar lauyoyinsa.
A ci gaba da kwan gaba kwan baya da huldar Jamhuriyar Nijar da wasu kasashen Yamma ke yi, kasar da ke karkashin mulkin soji, ta yi shelar yanke huldar soji da Amurka.
Paul Alexander ya rasu ranar Litinin yana da shekaru 78, a cewar wata sanarwa da dan'uwansa, Philip Alexander, ya fitar ta kafar sada zumunta.
Majalisar Wakilan Amurka ta zartar da muhimmin kudirin daka iya haramta amfani da manhajar Tik tok a kasar.
Hukumar Baitulmalin Amurka ta kakaba takunkumi ma mutane da hukumomi 16 a yankunan kuryar Afirka da Gabas ta Tsakiya.
Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken a Litinin din nan ya yi alkawarin karin dala miliyan 133 don tallafawa kasar Haiti, yana mai cewa, rikicin da ke kara kamari ya nuna butar gaggawa na tura dakaru na kasa da kasa.
An fara bikin Oscars na 2024 da Da'Vine Joy Randolph, wadda ta lashe lambar yabo ta farko a daren. Dama an yi hasashen za ta samu lambar yabon.
Shugaban Amurka, Joe Biden ya bude jawabinsa na shekara-shekara tare da sukar Trump kai tsaye kan gayyatar Shugaban Rasha Vladimir Putin da ya kai wa sauran kasashen kungiyar NATO hari idan ba su kashe kudi mai yawa kan tsaro ba.
'Yar Majalisar dattijan daga Alabama, Katie Britt, wadda ita ce 'yar jam'iyyar Republican mafi karancin shekaru da aka zaba a Majalisar dattijan Amurka, ta soki Shugaba Joe Biden da gwamnatinsa kan iyakoki, yanayin tattalin arzikin Amurka da batutuwan da suka shafi laifuffuka da tsaro a matsayin martani.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.