Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sake Kama Mutumin Da Ya Kashe Budurwarsa A Amurka Ya Bar Gawar A Mota Ya Tsere Kenya


An sake kama Kevin Adam Kinyanjui Kangethe
An sake kama Kevin Adam Kinyanjui Kangethe

An sake kama wani mutum da ake nema ruwa a jallo a jihar Massachusetts domin fuskantar tuhumar kisan kai, mako guda bayan ya tsere da dubara daga hannun ‘yan sanda, in ji ‘yan sandan Kenya a ranar Laraba.

WASHINGTON, D. .C. - Kevin Adam Kinyanjui Kangethe ya tsere ne a lokacin da yake jiran a mika shi kan sammacin Massachusetts bisa zarginsa da kashe budurwarsa tare da barin gawarta a mota a filin jirgin sama na birnin Boston. A makon da ya gabata ne ya zame daga ofishin 'yan sanda ya shiga cikin wata karamar mota.

An kama Kangethe ne a Embulbul, gundumar Kajiado da ke wajen babban birnin kasar Kenya a yammacin ranar Talata yayin da yake neman mafaka a daya daga cikin gidajen 'yan uwansa, in ji Shugaban 'yan sandan Nairobi Adamson Bungei.

Kevin Kangethe
Kevin Kangethe

"Mun sake kama shi kuma mun gode wa duk wadanda suka taimaka a wannan aiki," in ji shi.

An kuma dakatar da jami’ai hudu daga bakin aiki a ofishin bayar da rahoto a ranar da ya kubuce, suna jiran matakin ladabtarwa kuma suna iya fuskantar tuhuma.

‘Yan sandan jihar Massachusetts sun ce a farkon watan Nuwamba ne dai Kangethe ya bar gawar budurwarsa a mota a filin tashi da saukar jiragen sama na Logan inda bayan nan ya shiga jirgi zuwa Kenya.

Jami’an Massachusetts sun ce sun yi aiki tare da hukumomin Kenya domin gano shi, kuma an kama shi a wani kulob na rawa a ranar 30 ga watan Janairu bayan ya kwashe watanni uku yana gudun hijira.

Wani jami’in ‘yan sanda ya shaidawa AP cewa Kangethe ya ce ya yi watsi da ‘yancin zama ‘dan kasar Amurka.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG