Shugaban Amurka Donald Trump ya kira sanarwar da aka yi jiya Lahadi a matsayin ta tarihi ya kuma jinjina wa amincewar gaggawa da gwamnatin tarayya ta yi don yin amfanin da kwayoyin garkuwar da ke cikin jinin wadanda suka warke daga cutar coronavirus ya na mai ayyana cewa sinadarin zai ceci rayukan masu fama da cutar coronavirus da yawa.
Trump da sakataren lafiyar gwamnatinsa, Alex Azar, a wani taron manema labarai, sun lura cewa an sami raguwar mace-mace a ‘yan kasa da shekaru 80 wadanda ba a sanya musu na’urar taimakawa numfashi ba da kashi 35 cikin 100, wata daya bayan an basu wannan sinadarin a farkon lokacin da suka kamu da cutar. An yi amfani da sinadarin wajen jinyar dubban wadanda suka kamu da cutar COVID-19 A Amurka.
Jim kadan kafin kalaman na Trump, hukumar kula da abinci da magunguna ta Amurka ta sanar da bada umurnin yin amfani da kwayoyin garkuwar jikin amma ba a amince da su ba gada daya.
Facebook Forum