Zaman da za a yi da iyayen 'yan matan chibok.
Mai Fafutukar Ilimin Mata ta Kasar Pakistan Malala Yousafzai, Najeriya, Yuli 14, 2014
Shugaba Goodluck Jonathan yayiwa Malala Yousafzai alkawarin saduwa da wasu daga cikin iyayen yaran da ta’adda suka sace watani uku kennan. Malala tayi bukin cika shekaru 17 ranar litinin a Najeriya da alkawarin yin aikin ganin cewa an kubuto da ‘yan matan. Malala ta tsallake rijiya da baya alokaci da ‘yan Taliban suka harbe ta.
Biyo bayan ziyara da Malala ta kawo Najeriya daliban Chibok su biyar da suka samu suka kubuta daga hannun 'yan Boko Haram sun gana da ita a Abuja.
Jami’an gwamnatin Najeriya dana Amurka sunyi muhawara dangane da batun tsaro, musamman ma game da ceto daliban Chibok wadanda aka sace sama da kwanaki 87 kennan.
Tsofin hukumomin Najeriyar sun marwa shugaba Goodluck baya.
Bayan kwanaki tamanin da 'yan Boko Haram suka sace daliban Chibok har yanzu ba'a san makomansu ba domin babu wani tabbas da gwamnatin tarayya ta bayar a kansu.
Maharan da ake jin cewa 'yan Boko Haram sun kai farmaki kan Majami'u da wasu kauyuka a kusa da Chibok.
An kai harin ne kusa da Chibok garin da 'yan bindiga suka kama 'yan mata su fiye da 200 cikin watan Afrilu.
Yau fiye da watani biyu kennan.
Mambobin majalisar Wakilan Amurka sunyi kira da babban Murya ga Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya, akan ya mike, kuma ya mayar da hankali wajen daukan matakan da suka dace domin ceto daliban Chibok da ‘yan bindiga suka sace yau kwanaki 66 da shida kennan.
Tawagar ministar ta kunshi tsohon firayim ministan Biritaniya Gordon Brown da kuma wasu 'yan kasar Biritaniya.
Domin Kari