Ga dukkan alamu akwai takaddama tsakanin mahukuntan Najeriya wadanda ke tabbatarwa ‘yan Najeriya cewar an kusa gano inda ‘yan matan makarantar Chibok da ‘yan Boko Haram suka sace yau kusan watani uku kennan, da ‘yan kungiyar fafutukar ganin an ceto ‘yan matan, na {#Bring back our girls}.
Wannan kungiyar dai sun shafe fiye da wata biyu sun matsawa gwamnati lamba domin a samu akubuto da ‘yan matan.
Wannan matsayin yazo a daidai lokacin da majalisar kasa wanda ta kunshi tsofin shuwagabanin kasa da tsofin Cif joji-joji na Najeriya da shugabanin majalisar kasa da gwamnoni da sauran masu fada aji a gwamnati, sukayi wani taro inda suka baiwa shugaban kasa Goodluck Jonathan, goyon bayansu da amincewa ya doshi hanyar da ta kamata domin kubutar da wadannan yaran batare da an rasa rayukansuba.