WASHINGTON, DC —
Yau fiye da watani biyu kennan da aka sace ‘yan matan Chibok har yanzu babu labari,sace dalibai ya jawo hankulan jama’a da dama da kuma kafofin yada labarai.
Matakin da Gwamnati, ke cewa tana dauka har yanzu bai yi tasiri ba, domin babu wani abu takamaimai da Gwamnati zata iya nunawa cewa suna kokarin kubuto da wadannan dalibai.
Wasu daga cikin iyayen yaran da aka sace sun ce kusan wata biyu da wani abu bamu ji komai ba sun ce mana an kafa kwamiti,har yanzu ba wani sahihin labari.
Iyayen suka ce sun amince zasu yiwa sojojin in an turosu jagora zuwa cikin dajin amma har yanzu babu wadanda suka zo.