Mutane da ake kyautata zaton ‘yan bindiga daga kungiyar masu tsatsaurar ra’ayin addinin Islama da ka fi sani da Boko Haram, sun kai hari kan wasu majami’u masu yawa a yankin arewa maso gabashin Najeriya jiya lahadi, suka kashe akalla mutane 24.
Jami’ai a yankin da kuma shaidun gani da ido, sun ce ‘yan bindiga kan babura sun kai hari kan kauyukan da suke kusa da garin Chibok a jahar Barno. Shaidun gani da idon suna zargin sojojin Najeriya da sanyin jiki wajen daukan matakai nan da nan kan irin wadannan hare hare.
Babu dai wata kungiya ko mutum d a ya fito nan da nan ya dauki alhaki kai wadannan hare hare.
A cikin watan Afrilu kungiyar Boko Haram ta sace ‘yan mata su fiye da metan a wata makaranta dake garin Chibok. Jami’an gwamnati suka ce har yanzu ba a san inda fiyeda 219 na ‘yan matan suke ba.