A taron karya kumalla da Majalisar Wakilan Amurka ta shirya jiya a fadarta dake nan Washington D.C, Jakadan Amurka Robert P. Jackson daga Ma’akatar harkokin wajen Amurka ya fara da bayyana dalilan barkewar rigingimun Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya.
Game da batun daliban Chibok, Jakada Jackson yace “muna yin duk abinda zamu iya, amma a tunani na, akwai matukar muhimmanci in gaya muku cewa ko gwamnatin mu zata fuskanci kalubale, ita kadai tace zatayi kokarin ceto dalibai sama da 200. Muna gani yana da matukar muhimmanci a tattara bayanai da yawa, a yi shiri sosai, kuma gwamnatin Najeriya ta hada kai damu domin gani an ceto wadannan yara”.